✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da faɗuwar Dala har yanzu ba mu gani a ƙasa ba — Jama’a

Ba dalili ba ne suke cewa wai ai sun sayi kayansu lokacin da farashin Dala ya hau.

Farashin kayan masarufi na ci gaba da tsada duk da darajar da Naira ke ci gaba da samu a kasuwannin musayar kuɗaɗen kasashen waje, bayan dauki da Nairar ke samu daga Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Farashin Dalar Amurka da ya kai har kusan Naira dubu biyu a baya, ya ci gaba da sauka inda a farkon makon jiya ya kai ana sayar da Dala a kan Naira dubu daya a kasuwannin musayar kuɗi masu zaman kansu (BDC).

Sai dai kayayyakin masarufi da a baya ’yan kasuwa suka danganta tsadarsu da tashin Dalar, ya ki sauka kasa, lamarin da ya daure wa jama’a da dama kai.

Amma wasu ’yan kasuwa da Aminiya ta tuntuba sun ce an fara samun sauki a abubuwan da ake sarrafawa a nan gida kamar shinkafa da sukari da madara, a yayin da farashin fulawa kuma ya kara yin sama.

Binciken Aminiya ya gano cewa, buhun shinkafa ’yar gida mai nauyin kilo 50 da farashinsa ya kai Naira dubu 72 a kasuwannin irin su Suleja, ya dawo Naira dubu 66 a wannan mako.

Sai buhun sukari da ya kai Naira dubu 86, ya dawo Naira dubu 73.

A yayin da buhun madara na Dano da a baya ya kai Naira dubu 175, a yanzu ya karye zuwa Naira dubu 136 a Suleja.

Sai dai wani dan kasuwa a garin Kubwa mai suna Alhaji Saleh Lawan ya ce hakan bai rasa nasaba da gushewar hada-hadar sayyayyar watan azumin Ramadan.

Ya bayyana cewa yawancin kayayyakin abinci irin shinkafa da sukari da madara kan yi tashin gwauron zabo a farkon watan Ramadan lokacin da ake sayensu da yawa don raba wa mabuƙata.

Ya ce farashin kan sauka kafin karewar watan, inda ya ce saukowar farashin shinkafa da sukari da madara a yanzu, ba zai rasa nasaba da hakan ba.

Sai dai a lokaci guda, dan kasuwar ya bayyana mamakinsa da karuwar farashin fulawa a wannan mako, a lokacin da farashin Dala ke yin kasa, inda ya bukaci gwamnati ta binciki lamarin don jin hanzarin kamfanonin fulawa na yin haka.

Wata matar aure da ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce buƙatar fulawa na karuwa a wannan lokaci da ake sarrafa abubuwa da ita don bikin Sallah.

Yusuf Sa’ad wani mai shagon kayan koli a Babbar Kasuwar Kubwa da ke Birnin Tarayya Abuja, ya ce ba a samu saukowar farashi ba a kayayyakinsu da suke sarowa daga biranen Legas da Kano ko Aba.

Ya ce sai dai yana jin hakan bai rasa nasaba da nisan wuraren da ake dauko kayan, wato kasashen China da Indiya, inda ya ce lokaci bai yi ba da kayan da aka sayo da sabon farashin Dalar ya iso Nijeriya musamman la’akari da safarar jirgin ruwa da yawancin ake jigilar kayayyakin.

“A lokacin da Dala take tashi, suna kara mana farashin kaya ne a kasa da awa guda.

“Misali za ka sayi kaya a wuri guda a kan Naira dubu 200, amma bayan awa guda idan ka koma sai ka ji an yi karin farashinsa zuwa Naira dubu 300 bayan sun buga waya a inda suke sayowa.

“Wannan sabon farashin ne za su bukaci wanda ya sayi kayan ya biya matukar bai kai ga biyansu kudin ba,” in ji Yusuf.

Ya ce sai dai a yanzu da Dalar ta sauko, ’yan kasuwar na cewa sun yi sautun kayan ne da tsohon farashin Dala, kuma babu dalilin da za su sayar da shi a kan sabon farashin da zai kai su ga faduwa.

Muhammad Sani, wani mai harkar yadi da atamfa a Kasuwar Wuse da ke Abuja, ya ce kayansu da yawanci ke zuwa daga kasar China ta jirgin ruwa, na daukar tsawon watanni kafin ya iso.

Ya ce saboda haka ba abin mamaki ba ne farashin kayan ya ki sauka nan take bayan karyewar kudin waje.

Ya ce inda abin mamakin yake shi ne, kara farashin kudin kaya da ake fuskanta a lokaci guda, bayan tashin Dala, inda ya ce hakan gazawar gwamnati ce wadda ya zarga da barin ’yan kasuwa suna yin hakan ba tare da tsawata masu ba, ta hanyan kayyade farashi.

Farashin dabbobi da nama na ci gaba da hauhawa

A gefe guda kuma farashin dabbobi da nama na ci gaba da tashi inda kilon nama ya kai Naira 6,000 a wasu yankunan Abuja.

Faduwar Dala: Ba mu gani a kasa ba — Kanawa

Sanin kowa ne farashin kayan abinci da na masarufi sun yi tashin gwauron zabo sakamakon tashin da Dalar Amurka ta yi a kasuwar canjin kudade inda al’umma suka bayyana cewa ba a taba ganin irin wannan yanayi ba.

A wannan lokaci koda kayayyakin da ake sayarwa wadanda babu ruwansu da Dalar Amurka sai da farashinsu ya yi sama, kamar kayan lambu da na marmari da sauransu.

A baya dai sai da farashin Dalar Amurka ya kai kusan Naira dubu biyu a kasuwar canji inda bayan kiraye-kiraye da aka yi ta yi ga Bankin CBN kan ya shigo cikin lamarin don samun sauki ga al’umma ne aka samu Dalar ta rika yin kasa zuwa yanzu da farashinta ya koma Naira dubu daya da ’yan motsi.

Sai dai za a iya cewa a yanzu da aka sami faduwar Dalar ko mutane sun gani a kasa, ma’ana sun samu saukin farashin kayayyakin kamar yadda ake zato?

Malam Aminu Dala ya ce bai ga wani bambanci ba har yanzu domin a cewarsa a rediyo ne kadai farashin ya canza.

“Ni dai zan iya cewa a rediyo kaɗai muke jin wannan magana, domin ban ga wani sauyi a farashin kayyakain da nake saye ba. Kasancewar duk kayayyakin da nake saye haka farashinsu yake babu wani sauyi,” in ji shi.

Wata matar aure mai suna A’isha Bashir ta ce babu wani sauyi da mutum zai ce ya gani kai-tsaye sakamakon faduwar Dalar.

Ta ce, “A gaskiya ba zan ce ba a samu sauyi gaba daya ba, domin a wasu kayayyakin abinci kamar su masara da gero da wake farashinsu ya dan sauka ba kamar baya ba.

Sai dai kayan abincin masu tsadar har yanzu farashinsu bai sauya ba idan ka ɗauki shinkafa da sukari da man girki.

“Kowa ya san cewa a daidai lokacin da Dala take tashi a kullum, haka farashin wadannan kayan abinci ya rika tashin gwauron zabo.

“Amma abin mamaki yanzu da Dalar ta fadi sai ga shi ’yan kasuwar sun yi shiru da bakinsu. Wannan abu ne da bai dace ba.”

Wani magidanci da Aminiya ta tattauna da shi ya ce babu wani sauyi da suka gani game da faduwar Dalar.

“Bayan an ce Dala ta fadi da na je kasuwa sai na tarar da farashin kayayyakin bai sauya ba.

“Da na yi magana da wani mutum da ke sayar da kayan abinci a kasuwa game da faɗuwar Dalar sai yake gaya min cewa wai shi ba da Dala yake sayen kayayyakinsa ba don haka babu ruwansa da batun tashi da saukar Dala.

“Kuma na san ƙarya yake yi domin lokacin da farashin Dalar yake tsaka da tashi, da zarar mutum ya yi korafi game da tashin farashin kayayyaki suna nuna cewa ba laifinsu ba ne wai Dala ce ta tashi,” in ji shi.

Yawancin mutanen sun nemi mahukunta su shigo cikin lamarin don tabbatar da cewa ’yan kasuwa suna sayar wa al’umma kaya cikin sauki tunda an samu faduwar Dalar.

Haka kuma sun yi kira ga ’yan kasuwar su ji tsoron Allah su sassauta farashin kayayyakinsu don jama’a su samu sauki musamman ma a wannan wata na azumin Ramadan.

“Ba abin da za mu iya yi game da wannan hali illa mu yi kira ga ’yan kasuwa su ji tsoron Allah su sani cewa za su mutu.

“Su duba su gani cewa lokacin da Dala ta tashi sun kara farashin kayayyakinsu wanda a kan haka mutane suka rika saye.

“A yanzu kuma da Dala ta fadi ya kamata su saukar da farashin kayayyakin.

“Ba dalili ba ne suke cewa wai ai sun sayi kayansu lokacin da farashin Dala ya hau idan sun dubi lokacin da Dalar ta tashi suna da tsofaffin kaya amma haka suka rika sayar da kayayyakin nan a kan sabon farashi,” in ji Malama A’isha Bashir.

Ta kara da cewa “Ina kira ga hukumomin gwamnati da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin ’yan kasuwa sun sauke farashin kayayyakinsu a wannan lokaci da aka samu faduwar Dalar Amurka.

“Gwamnati tana da karfi sosai za ta iya tilasta wa ’yan kasuwa su sauke farashinsu ta hanyar hadin kai da shugabannin kasuwanni.

“Duk wanda kuma aka same shi da karya doka to ya kamata a hukunta shi daidai da laifinsa.