✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Duk da daliget din Kogi 63, kuri’a 47 Yahaya Bello ya samu

Ko da yake ba za a iya cewa duk kuri’un da ya samu sun fito ne daga daliget din jiharsa ba.

Gwamnan Jihar Kogi ya tas hi da kuri’a 47 a zaben fid-da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC.

Yaya Bello wanda ya ki amincewa da janyewar ’yan takarar Arewa a zaben ya samu kuri’a 47 ne duk da cewa daliget 63 suka kada kuri’a daga Jihar Kogi da yake jagoranta.

Ko da yake ba za a iya cewa duk kuri’un da ya samu sun fito ne daga jiharsa ba.

Duk da haka, his ne na hudu wajen yawan kuri’un da aka jefa a zaben da ya gudana a dandalin Eagles Square da ke Abuja.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma Uban Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Ahmed Tinubu, shi ne ya lashe zaben da fiye da rabin kuri’un da aka jefa.

Daliget sama da 2,340 ne suka jefa kuri’a a zaben, uku daga kowacce daga kananan hukumomi 774 a jihohi 36 da kuma shida a yankin Birnin Tarayya.