✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun ’yan fashin da suka addabi yankin Karu ta cika

’Yan Sanda sun damke wasu da ake zargin ’yan fashi ne su uku da suka addabi al’ummar yankin Karamar Hukumar Karu na Jihar Nasarawa. Kakakin…

’Yan Sanda sun damke wasu da ake zargin ’yan fashi ne su uku da suka addabi al’ummar yankin Karamar Hukumar Karu na Jihar Nasarawa.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa jami’ansu sun kwace bindigogi da  wata motar sata a hannun ’yan fashin.

Sanarwar da ya fitar a ranar Talata ta ce, “’Yan sanda da ke aiki karkashin ofishin yankin New Karu, sun samu nasarar damke Musa Mohammed da Adams Lawal da kuma Mark Friday.

“An gano kananan bindigogi kirar gida guda biyu da alburusai sai kuma mota kirar Honda Accord da suka kwace a hannun wani mutum a kauyen One Man village.

“Binciken farko ya nuna wadanda ake zargin ’yan fashi da makami ne wadanda suka shahara wajen kwace motocin jama’a.

“Haka nan, binciken ya yi silar kama wani mai suna Kayode Olajide, wanda shi ne mai sayen motocin sata daga ’yan fashin,” in ji shi.