✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun wasu barayin motar dan majalisa ta cika a Katsina

Matasan sun yi fashi ne a gidan dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Kangiwa a Jihar Kebbi.

Da Yammacin ranar Litinin ne Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta gabatar da wasu matasa biyu da take zargi da aikata fashi da makami.

Ana zargin matasan ne da yin fashin ne a gidan dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kangiwa a Jihar Kebbi, Hon. Umaru Abdullahi Zimbo a Abuja.

A cewar Kakakin Rundunar, SP Gambo Isa, “Mun samu rahoton sirri cewa su wadannan ’yan fashi kimanin su bakwai sun je gidan dan majalisar da misalin karfe bakwai na safe.

“Sun yi harbe-harbe sannan suka kwashi kaya ciki har da na’urar Laptop, sannan suka yi awon gaba da motar shi kirar Prado Jeep wadda suka musanya wa lamba daga HMHR 267A zuwa ABC 79 GC,” inji shi.

Ya ce sashen yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar ne ya kamo matasan a kan hanyarsu ta shiga Jamhuriyar Nijar daf da kan iyakar Jibiya.

Ya ce jami’an sun samu nasarar hakan ne bayan harbin tayar motarsu a lokacin da matasan suka ki tsayawa yayin da aka tare su a hanya.

Matasan da suka shiga hannu su hada da wani mai shekara 38 mazaunin Kurmin Mashi ta Jihar Kaduna, dayan kuma mai shekaru 30 da ke Karshen Waya a unguwar Gyadi-Gyadi a Jihar Kano.

“Sun shigo ta Katsina ne bayan sun yi badda-kama ta shigar manyan kaya a kan hanyarsu ta zuwa kai wannan mota ga wani mutumin Maradi a Jamhuriyar Nijar mai suna Garba kamar yadda suka ambata,” inji kakakin.

Daya daga cikin wadanda aka kama ya ce duk da cewa ba da shi aka yi satar ba, amma ya san motar sata ce kuma wannan shi ne karonsa na farko na shiga wannan.

A cewarsa wani daga Abuja ne ya zo da motar wadda suka sanya wa na’urar hana gano inda take (Anti-tracking device).

“Sun wuce Kano inda shi wancan na Abuja ya yi bankwana da su yayin da suka kamo hanya tare da Jamilu wanda a cewarsa shi ne wanda ya san hanya kuma ya san mutumin da za su hadu da shi a nan kan iyakar Jibiya.

“Jamilu ya ce, an yi da shi za a bashi Naira dubu 100 idan sun kai wannan mota,” inji shi.

SP Gambo ya ce za su ci gaba da bincike har su kamo ragowar mutane biyar daga cikin bakwai din.