✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun wanda ya yi wa ’yar shekara 10 fyade ta cika

Wani mai shekara 45 da ya yi wa wata yarinya mai shekara 10 fyade a cikin wani kango ya shiga hannu.

Wani mai shekara 45 da ya yi wa wata yarinya mai shekara 10 fyade a cikin wani kango ya shiga hannu.

A ranar Talata ne ’yan sanda suka cafke mutumin, inda suka gano ya yaudari yarinyar ne zuwa wani kangon ya yi mata fyade, daga baya ya ba ta Naira 100.

Kakakin  Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta bayyana cewa “mutumin ya ce kullum yarinyar da kawarta kan zo wajensa su karbi N100, rannan da ta zo karba ne ya shigar da ita cikin kangon ya yi lalata da ita.”

Ta ce rundunar ta kuma cafke wani wanda ya yi amfani da kayan sojoji ya yi wa wata mata fashin N1,203,000 a Jihar Osun.

Wanda ake zargin ya kuma yi fashi wayar iPhone Promax 13/14 da dan kunnen zinare na da kudinsa ya kai N350,000 da kuma kudi N73,000.

ta ce nan gaba za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.

%d bloggers like this: