Rundunar ’yan sandan Najeriya ta gabatarwa manema labarai wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane 31 da kuma fashi da makami a kan hanyar Abuja zuwa Minna da kuma hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan, CSP Jimoh Moshood wanda ya gabatar da wadanda ake zargi a kauyen Dikko kusa da garin Suleja da ke Jihar Neja a ranar jiya ya ce biyar daga cikin wadanda ake zargi sun mutu a musayar wutar da suka yi da jami’an ’yan sanda.
Ya ce sai dai su ma ’yan sanda sun rasa daya daga cikinsu mai suna Saja Shettima Abdullahi yayin da batagarin suka yi musu kwantan-bauna a safiyar ranar 26 ga watan Satumban shekarar 2017.
Ya bayyana cewa sun kama bata-garin ne a maboyarsu da kuma sansaninsu inda ’yan sanda suka kubutar da mutanen da batagarin suka yi garkuwa da su.