Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta ce ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da kwarewa wajen yin fashi a wajen cirar kudi na POS a jihar.
Wadanda ake zargin su biyu dai sun yi wa wata mata mai suna Jummai Maryam Bashir a Lokoja fashin kudi N50,200, a ranar Alhamis.
- Babu wanda zai bar jami’a don bai biya kudin makaranta ba — Farfesa Sani Tanko
- FGC Yauri: Dalibi ya rasu yayin artabun sojoji da ’yan bindiga
Rundunar ta bakin kakakinta a Jihar, ASP Williams Avye Aya, ta ce wadanda ake zargin sun ruda matar da suka yi wa fashin kudin.
Bayan wani lokaci ta gane cewar mutum biyun sun cuceta, sai ta ja hankalin mutane, inda ba jimawa aka cafke su suna shirin shiga Abuja.
Kakakin ’yan sandan jihar ya kuma ce bayan cafke su, N43,200 kacal aka samu a wajensu.
Wadanda ake zargin sun amsa aikata laifin, sannan suka ce sun kuma aikata fashi da makami a garin Jalingo, Makurdi da kuma Otukpo.
Sanarwar rundunar ’yan sandan ta ce ana ci gaba da bincike don cafke ragowar abokan aikin nasu.