Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta cafke wani tsoho mai kimanin shekaru 70 a duniya bisa zargin yin safarar miyagun kwayoyi ga ’yan ta’addan Boko Haram da kuma ’yan bindiga a jihar Neja.
Kakakin hukumar, Mista Femi Babafemi wanda ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Asabar a Abuja ya kuma ce wanda ake zargin dan asalin garin Dallawa ne a jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar.
- An karrama kamfanin giya a matsayin wanda ya fi kowanne biyan haraji a Kaduna
- Fashewar bam ta tarwatsa masu zabe a Abiya
Ya ce an kama shi ne a garin Jebba na jihar Neja ranar Alhamis da kulli 10 na miyagun kwayoyin.
Kakakin ya ce asali mutumin ya kawo fatu da kiraga ne daga Nijar domin sayarwa a jihar Legas.
“Yayin da muke bincike a kansa, ya yi ikirarin cewa ya sayar da kayansa ne a kan kudi N300,000 sannan ya yi amfani da kudin wajen sayen kulli 10 na miyagun kwayoyin, kowanne a kan N25,000.
“Yana kan hanyarsa ta komawa Nijar dinne ta jihohin Arewa maso Yamma a inda yake tsayawa ya sayar da kwayoyin ga ’yan bindiga lokacin da muka kama shi a Jebba,” inji Mista Femi.
Ya kuma ambato Kwamnadan hukumar a jihar ta Neja, Aloye Isaac wanda ya ce kamun ya kara tabbatar da alakar da take tsakanin ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.