Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wani mutum da ake zargi da bai wa ’yan bindiga bayanai a yankin Tafa da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko a jihar.
Mutumin mai suna Abubakar Yahuza mai shekara 36, wanda ke zaune a Gidan Abeh da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko a jihar.
- Tinubu ya kori Arabi, ya naɗa Usman a matsayin shugaban NAHCON
- ’Yan sanda sun kama mutum 2 da AK-47 a Zariya
Wanda ake zargin ya tabbatar da cewa yana bai wa masu garkuwa da mutane bayanai domin tsara yadda za su sace waɗanda ƙaddara ta faɗa musu.
Har wa yau, rundunar ta yi nasarar ceto wasu manoma biyu a garin Kuriga da ‘yan bindiga suka yunƙurin sace su a gonakinsu.
Rundunar ta yi artabu da maharan, wanda hakan ya kai jikkata mutum biyu, wanda aka kai su asibiti tare da yi musu magani.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Audi Ali Dabigi, ya yaba wa jami’an rundunar kan yadda suka nuna ƙwarewa a lokacin da suka ceto mutanen.
Kazalika, Kwamishinan ya tabbatar wa jama’ar jihar cewar rundunar za ta ci gaba da kare su da kuma dukiyoyinsu.