✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubai ta soke harajin barasa domin zawarcin masu yawon bude ido

Sai mutum yana da lasisi na musamman zai sayi barasa a Dubai.

Hukumomin Dubai sun soke harajin da ake biya na kashi 30 cikin dari na sayen barasa a wani yunkuri da ake gani na kokarin zawarcin ’yan yawon bude idanu ne.

Haka kuma jama’a za su daina biyan kudin harajin da suke bayarwa na ka’ida na samun izinin shan giyar a gida, wanda sai sun yi haka ne suke da damar sha ba tare da cewa sun keta doka ba.

A baya-bayan nan Dubai na ta sassauta dokokinta inda take bayar da damar sayar da barasa a fili kuma a rana tsaka hatta a cikin watan azumi na Ramadan, tare kuma da amincewa da kai barasar gidaje ga mabukata a lokacin annobar Coronavirus.

Ana ganin duka wadannan matakan da hukumomin ke dauka wani kokari ne na jan ‘yan kasashen waje birnin domin gogayyar da suke fuskanta daga makwabtan kasashe.

Kamfanoni biyu da ke hada-hadar barasa a birnin na Dubai, Maritime and Mercantile International (MMI), da kuma African & Eastern, sun ce za su rage farashin barasar sakamakon cire musu harajin da aka yi.

Kakakin kamfanin MMI, ya yaba da matakin, inda ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na AP, cewa, “Tun da muka fara harkokinmu a Dubai sama da shekara 100 da ta gabata, matakan da masarautar ke dauka abin a yaba ne domin tana la’akari da zamani tare da kokarin tafiya da kowa.”

Ya ce, “Wadannan sauye-sauye da aka yi a kan dokokin za su tabbatar da masu bukata na saye da shan barasar hankali kwance ba tare da wata fargaba ba a Dubai da Hadaddiyar Daular Larabawan gaba daya.”

Sai dai ya ce ba su sani ba ko matakin hukumar da ya fara aiki ranar Lahadi zai kasance na dindindin.

Jaridar Financial Times ta bayyana matakin da cewa na gwaji ne na shekara daya, inda ta alakanta majiyarta da manyan jami’an harkokin kasuwanci.

Kamfanonin barasa sun ce za su rage farashi saboda cire harajin

Ma’aikata ‘yan kasashen waje sun ninka ‘yan kasa tara a Dubai, kuma mazauna birnin da ke shan barasa yawanci suna tafiya Umm al-Quwain da sauran birane domin sayen barasa mai yawa idan suna bukata.

Daman shi birnin Dubai yana samun ‘yan yawon bude idanu da attajiran ma’aikata ‘yan waje fiye da makwabtansa, galibi saboda sassaucin dokokinsa.

To amma a yanzu birnin na fuskantar gogayya daga wasu daga cikin makwabtan kasashe da birane, inda suma suka tashi domin bunkasa harkokinsu na yawon bude idanu da bangare samun kudadensu.

Duk wanda ba Musulmi ba ne da ke zaune a Dubai dole ya kasance ya kai shekara akalla 21, kafin ya sha barasa ko ya yi safararta ko ya ajiye ta a gida, sannan kuma dole ne ya kasance ya samu takardar izinin hakan – wanda wani kati ne na musamman na roba da ‘yan sanda ke bayarwa.