Hukumar tsaro ta DSS ta ce tana shirin fara kerawa da sayar da jirage marasa matuka ga sauran hukumomin tsaron Najeriya.
Daraka-Janar na hukuar DSS, Yusuf Bichin ya ce nan ba da jimawa ba, za a kaddamar da makaman da jami’an hukumar suka kera.
Shugaban hukumar ya sanar da haka ranar Asabar a bikin yaye malarta kwas din binciken kwakwaf a babban matakin gudanarwa.
Hakan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-ce bayan wani jirgi mara matuki na Rundunar Sojin Kasa ta kasar ya jefa wa farare hula bom ya kashe mutane 120 bisa kuskure.