✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta tsare Omoyele Sowore

Za a gudanar da zanga-zanga daga ɗaya ga watan Oktoba zuwa abin da ya sawwaƙa.

Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun cafke fitaccen madugun gwagwarmayar nan na Nijeriya, Omoyele Sowore.

Omoyele ya shiga hannu ne a yau Lahadi a Filin Jirgin Saman Murtala Mohammed da ke Legas jim kaɗan bayan shigowarsa Nijeriya.

Cikin wani saƙon hoto mai ɗauke da rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore ya ce Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta kuma ƙwace fasfo ɗinsa.

“Ina sauka a filin jirgi na MMIA a Legas daga Amurka, sai jami’an Hukumar NIS suka ƙwace fasfo ɗina tare da shaida min cewa an ba su umarnin su tsare ni.

“Sai dai wannan ba abin mamaki ba ne la’akari da yadda na riga na san Gwamnatin Bola Tinubu da take haƙƙin masu da adawa da ita musamman kan fargabar da take yi wa zanga-zangar juyin juya halin da ke tafe a watan Oktoba.

“Idan shi ma wannan kamen tare da tsare ni ya ɗauki tsawon lokaci, ina mai kira ga dukkan ’yan ƙasa da su yi amfani da duk wata hanya da ta dace wajen gudanar da zanga-zangar da za a gudanar daga ɗaya ga watan Oktoba zuwa abin da ya sawwaƙa.”

Sai daga bisani mahukuntan sun saki Sowore, inda ya sake wallafa cewa, “yanzun nan hukumar shige da fice ta Nijeriya ta sake ni bayan tsare ni wani taƙaitaccen lokaci. Sun kuma ba ni fasfo ɗina.”

Wannan kamen da Gwamnatin Nijeriya ta yi wa Omoyele Sowore ba shi ne farau ba, inda a shekarun bayan nan ya shiga hannun mahukuntan ƙasar kan zarginsa da cin amanar ƙasa.

A shekarar 2019 Omoyele Sowore ya shafe aƙalla watanni uku a hannun Hukumar DSS kan jagorantar zanga-zangar juyin juya halin ta Revolution Now.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Hukumar ta DSS ta saki Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC, Kwamared Joe Ajaero bayan kama shi da ta yi.

DSS ta cafke Ajaero ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin da yake hanyarsa ta zuwa wani taron ƙungiyoyin kwadago a Birtaniya.