Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a zaɓen 2023, Omoyele Sowore, ya ce an tsare shi na ɗan lokaci a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas bayan dawowarsa daga Amurka.
Sowore, ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter) a safiyar ranar Lahadi, inda ya ce an sake shi bayan shafe mintuna kaɗan a hannu jami’an tsaro.
- Yadda mafi lalacin kulob ya yi nasara ɗaya cikin shekara 20
- Yadda Masarautar Kaltungo ke yakar yunwa da fatara — Mai Kaltungo
Sowore, wanda ya jagoranci zanga-zangar #RevolutionNow, ya ce jami’an shige da fice na Najeriya, sun ƙwace masa fasfo tare da shaida masa cewa an ba su umarnin tsare shi.
“Na iso Najeriya daga Amurka a filin jirgin sama na Legas; da na isa wajen jami’an shige da fice, sun ƙwace min fasfo suka ce an ba su umarnin tsare ni.
“Ba abin mamaki ba ne, domin na daɗe da sanin cewa wani ɓangare ne na mulkin kama-karya da gwamnatin Tinubu ke yi kan masu sukarta, da tsoron zanga-zangar #FearlessINOctober da ke tafe.
“Idan tsarewar ta ɗauki lokaci, ina kira ga ’yan Najeriya su tabbatar sun daƙile zalunci ta kowace irin hanya da ta dace, ta hanyar yin zanga-zanga daga ranar 1 ga watan Oktoba.
“Yanzu haka an sake ni bayan tsarewar da jami’an shige da fice suka yi min, kuma sun dawo min da fasfo ɗina,” in ji shi.
Sai dai har zuwa yanzu ba a tabbatar da wanda ya bayar da umarnin tsare shi ba.
Amma rahotanni sun nuna cewar jami’an hukumar tsaro ta DSS ne suka kama shi.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, DSS ba ta tabbatar da ko musanta kama Sowore da jami’anta suka yi ba.