Dubun wasu masu cibiyar rajistar katin zabe na karya ta cika, inda jami’an hukumar tsaro ta DSS suka cafke su suna damfarar mutane.
’Yan damfarar sun shiga hannu ne bayan sun bude cibiyar rajistar katin zabe ta karya, suna tsaka da karbar kudaden mutane tare da yi musu alkawarin samun katin zabe a Kananan Hukumomi 13 da ke fadin Jihar Nasarawa.
- INEC ta cire sunan Ahmad Lawan daga jerin ’yan takarar 2023
- Mai neman takarar Sanatan Yobe ta Arewa ya maka Machina a Kotu
Shugaban Sashen Wayar da Kan Jama’a na INEC reshen Jihar Nasarawa, Ibrahim Anawo, ya ce mutanen, “Suna karbar N1,000 a kan kowane mutum daya, idan ka kiyasta kudaden da suka karba daga hannun mutane suna da yawa.
“Irin wadannan ne suke bata wa Hukumar INEC suna kuma ba za mu lamunta ba. DSS za ta mika wa ’yan sanda kes din domin ci gaba da bincike”.
Jami’in ya bayyana cewa DSS ta kama mutanen ne a lokacin da suke tsaka da raba wa mutane fom din yin rajistar zabe da nufin karbar kudadensu a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Lafia, hedikwatar jihar.
Ibrahim Anawo ya bayyana cewa mutanen sun shiga hannu ne ta hanyar bayanan sirri da kwamitin da hukumar ta kafa domin bincike kan zargin tatsar kudade daga hannun masu neman rajistar zabe a jihar ya samu.
Ya ce, “Wadanda ake zargin suna ikirarin cewa kungiyarsu, wato Kungiyar Matasa Domin Cigaban Yankin Middle Belt ta yi hadin gwiwa da INEC, shi ya sa suke yi wa masu zabe rajista.
“Sun rubuto mana wasikar bukatar hakan daga kungiyar amma ba mu amince musu ba; to me ya sa za su je su rika karbar kudaden jama’a har suna cewa suna da hadin gwiwa da INEC?” In ji shi.