✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta kama wadanda suka yi wa daliba fyade har ta mutu

Za a gurfanar da su a gaban kuliya ranar Laraba.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama mutum takwas kan zargin yi wa wata daliba fyade har sai da ta mutu.

DSS ta ce an tsinci gawar Olajide Blessing ne a gidanta an daure bakinta kafin a yi mata fyade har ta mutu.

A lokacin da aka tsinci gawar dalibar, wadda ke aji uku a fannin ilimin noma na Jami’ar Ilorin, an samu jikinta da raunuka.

Fyaden da aka yi mata har ta mutu ya haifar da zanga-zanga a fadin Najeriya inda kungiyoyin fararen hula suka yi ta kira da a kamo sannan a hukunta wadanda suka yi mata aika-aikan.

Majiyoyinmu a hukumar DSS da suka bukaci kar a bayyana sunayensu sun tabbatar da kama wadanda ake zargin, wadanda suka ce suna taimaka wa hukumar wajen bincike.

Mun nemi samun karin bayani daga mai magana da yawun hukumar DSS, Nnochirionye Afunanya, amma ya ce sai dai mu tura masa da rubutaccen sakon waya.

Sai dai kuma har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto bai amsa sakon da muka tura masa ba.

Amma Darekta Gurfanar da Masu Laifi na Jihar Kwara, Mumini Jimoh (SAN), ya tabbatar mana da kama wadanda ake zargin, kuma za a gurfanar da su a gaban Mai Shari’a I.A. Jusuf a ranar Laraba.