Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama wata matashiya da ta yi barazanar tayar da bam domin kashe Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da alkalan kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar Kano.
Matashiyar, mai suna Fiddausi Ahmadu, mai shekara 23, ’yar unguwar Dandinshe da ke Kano, yanzu haka tana hannun hukumar, kamar yadda wata majiya a hukumar ta tabbatar.
Majiyar ta ce da zarar an kammala bincike a kan ta, za a gurfanar da ita a gaban kotu.
A cikin wani bidiyo dai da ya karade kafafen sada zumunta, an ga Fiddausi na caccakar dukkan wadanda suke da hannu a nasarar da kotun ta ba Nasiru Yusuf Gawuna a hukuncin da ya soke nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Kano, tare da barazanar kashe su.
An gan ta tana barazanar dasa bam domin kashe Kashim Shettima da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje da Gawunan da kuma alkalin da ta jagoranci yanke hukuncin.
Ta yi barazanar cewa a duk inda ta gan su, za ta iya dasa bam ta rungume su su mutu tare.
Majiyoyi dai a hukumar sun tabbatar da kamun nata.
“Tabbas mun kama Fiddausi Musa Ahmadu kuma za mu kai ta kotu, saboda wannan barazanar da ta yi ba za mu dauke ta da wasa ba,” in ji majiyar.
Kazalika, iyayenta da ’yan uwanta ma sun tabbatar da kamun nata, amma suka nemi a yi mata afuwa.
A cewar mahaifiyarta, “Jami’an tsaro dauke da manyan makamai sun zo gidanmu cikin dare sun tafi da ita.
“Tabbas ta yi kuskure, amma muna roko a madadinta da a yi mata sassauci, ba za ta kuma ba. Muna son ta dawo gida, muna bayar da hakuri,” in ji mahaifiyar Fiddausi.