✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar Amurka ta fitar da takardun karatun Tinubu

Atiku na zargin takardar shaidar karatun Jami'ar Jihar Chicago (CSU) da Tinubu ke amfani da ita ta bogi ce

A karshe Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka ta fitar da takardun shaidar karatun Shugaba Bola Tinubu kamar yadda dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya nema.

A ranar Litinin Jami’ar CSU ta fitar da takardar shaidar karatun Shugaba Bola bisa umarnin kotun da ke yanin Illinois a Amurka, inda Atiku ya shigar da karar, domin samun takardun a matsayin hujjar zargin da yake wa Tinubun da amfani da takardun bogi.

Atiku ya shigar da kara kotu yana kalubalantar nasarar Tinubu a zaben 2023 kan dalilan da suka hada da zargin Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zaben ta Najeriya (INEC) takardun shaidar karatu na bogi domin tsayawa takara.

Takaddamar shaidar karatun Tinubu ta dade tana tayar da kura a fage siyasaar Najeriya, musamman a zaben na 2023, inda Atiku ke zargin wanda sunansa ke kan takardar da Tinubu ya gabatar wa INEC mace ce ba namji ba.

Atiku wanda ke neman kotu ta soke nasarar Tinubu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ya garzaya kotun Amurka ne bayan hukumar gudanarwar Jami’ar CSU ta sanar cewa Tinubu tsohon dalibinta ne da ya kammala digirinsa a shekarar 1979.

Hakan kuwa ta faru ne bayan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya ta kori zargin takardun bogin da Atikun ke wa Tinubu, wanda kotun ta ce dade da yanke hukunci a kan ingancinsu tun a lokacin da Tinubun yake gwamnan jihar Legas.

Amma bisa rashin gamsuwarsa da hukuncin da ya daukaka kara, ya garzaya kotun Amurka yana neman aininhin takardu da kuma bayanan karatun Tinubu.

Sai dai a lokacin da hukumomin jami’ar sun ce ba su da hurumin fitar da bayanan karatun wani mutum, sai bisa umarnin kotu, domin kuwa bayanan karatun dalibi abu ne da ya kebanci alfarmarsa ta kashin kai.

Aminiya ta kawo rahoton cewa wani mai sharhi kan al’amarun yau da kullum, Durojaiye Ogunsanya, ya bayyana cewa ajinsu daya da Tinubu a Jami’ar CSU, tare suka kammala a 1979, inda ya ce a lokacin Tinubun shugaban kungiyar daliban sashen aikin akanta, kasuwanci da mulki.

Kotu ta yi watsi da bukatar Tinubu

A yayin da Atiku ke naman takardun Tinubu, shi ma Tinubu ya shigar da bukatar hana izinin fito da takardun shaidar karatun domin abu ne da ya kebance shi.

A ranar Asabar Mai Shari’a Nancy Maldonado ta yi watsi da bukatar Tinubu ta ba da umarnin fito da bayanai da takardun karatun cikin sa’a 48.

Alkalin ta bayyana cewa muhimmancin batun ya zarce alfarmar Tinubu, tun da ya gabatar wa INEC takardar shaidar karatun nasa domin tsayawarsa takarar shugaban kasa kamar yadda dokar zaben Najeriya ta tanada.

Ta ce hasali ma, a matsayin Atiku na dan takarar shugaban kasa a zaben na 2023, ya bukaci takardun ne domin gabatar da shaida a karar ya daukaka a Kotun Koli cewa Tinubu bai cancanci tsayawa takara ba.

Jami’ar CSU ta fito da takardun karatun Tinubu

Bayanan karatun da lauyan Jami’ar CSU Michael D. Hayes, ya fitar sun suna ya kammala karatun Digiri a 1979, sai dai sunan bai fita sosai ba, wanda jami’ar ta bayyana cewa saboda kare hurumin dalibi ne.

Ba mu ga takardar diflomar Tinubu —CSU

Jami’ar at kar da cewa ta kasa gano ainihin takardar shaidar diflomar Tinubu a 1979, wanda a baya ta bayyana cewa ba takardar ba ta cikin muhimman takardu, abu ne kamar na al’ada da ya kebanci dalibai.

Ta ce, “CSU ba ta ajiye kwafin shaidar diflomar dalibai, kuma mun yi duk neman da za mu iya mun kasa ganin kwafin shaidar diflomar Tinubu a 1979,” kamar yadda aka bukata.

Atiku ya bukaci irin kwafin shaidar diflomar da aka ba wa Tinubu a 1979, wanda CSU a bayar amma at ce, “An rufe sunan dalibin saboda kare huruminsa. CSU za ta samar da kwafin shaidar da za a maye gurbin wadda aka ba wa Tinubu a ranar 27 ga Yuni, 1997.”

Atiku ya yi gum

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Atiku ka sakin takardun na Tinubu ta wayar tarho, amma kakakinsa, Phrank Shaibu, ya ce zai nemi wakilin namu daga baya.

Sai dai har zuwa misalin karfe 12 na dare da aka kammala wannan rahoton bai nemi wakilin namu ba, kuma bai amsa rubutaccen sakon da wakilin namu ya tura masa ba.

%d bloggers like this: