✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta kama buhu 2,000 na shinkafar tallafin da aka karkatar a Katsina

Jami'an DSS sun iske shagunan mutanen cike da shinkafar tallafin d a Gwamnatin Tarayya ta bayar a raba wa talakawan jihar

Hukumar tsaro ta DSS ta kama sama da buhu 2,000 na shinkafar tallafin Gwamnatin Tarayya ta bayar a raba wa talakawa a hannun wasu da ake zargin sun karkatar ne a Jihar Katsina.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamnatin Tarayya ta ba da tirela 20 na shinkafa domin raba wa talakawa, da nufin rage musu radadin yunwa da tsadar rayuwa.

Jami’an DSS sun kama wadanda ake zargin sun karkatar da shinkafar da ya kamata a raba wa talakawan jihar ne a Babbar Kasuwar Katsina.

A daren ranar Laraba ne DSS ta kama ’yan kasuwan da ake zargi, inda jami’an hukumar suka iske shagunan mutanen cike da shinkafar tallafin.

Wasu dai na zargin ba za a rasa  hannun wasu jami’an gwamnati a wannan badakalar ba.