Hukumar tsaro ta DSS ta sanar cewa ta cafke wanda ake zargi ya jagoranci dana bom din da ya tashi a yayin da Shugaban ke ziyarar aiki a Jihar Kogi.
A ranar 29 ga Disamba, 2022 ne bom ya tashi kusa da Fadar Sarki Ohinoyi na Kasar Ibira a Okene, Jihar Kogi yayin da Shugaba Buhari ke ziyarar aiki a masarautar.
- Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin manoma 20 a Kebbi
- An kama mai gyaran wuta a cikin likitocin bogi masu aiki a asibitoci fiye da 100 a Kano
Cikin sanarwar da ta fitar ranar Laraba a Abuja ta bakin kakakinta na kasa, Peter Afunanya, hukumar ta ce “Yayin binciken an gano wanda aka cafken babban kwamanda ne a ISWAP.
“Ya jagoranci ko yana da hannu a hare-haren da aka kai ofishin ’yan sanda a Karamar Hukumar Okehi, Jihar Kogi a 2022 inda jami’i daya ya rasa ransa.
“Shi ne kuma ya kitsa Harin Gidan Yarin Kuje a Abuja a watan Yuli da kuma harin da aka kai kamfanin WACL a Ajaokuta duk a shekarar 2022.
“Ana kuma zargin sa da hannu a harkar satar mutane a jihohin Kogi da Ondo,” in ji hukumar.
Afunanya ya ce ana tsare da wanda ake zargin tare da wanda ta kama su tare, kuma za a gurfanar da su a kotu nan gaba kadan.
Ya jadadda cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyar al’uma kamar yadda ya rataya a kanta.