✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

DSS na neman Sunday Igboho ruwa a jallo

DSS to ce samamen ya biyo bayan samun bayanan sirri kan gidan.

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS da yammacin ranar Alhamis ta tabbatar da kai samame gidan Bayaraben nan mai fafutukar ballewa daga Najeriya, Sunday Igboho tare da bayyana nemansa ruwa a jallo.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa da misalin karfe 1:34 na daren ranar ta Alhamis, wani ayarin jami’an tsaro sun yi wa gidan dan tawayen kawanya da ke yankin Soka a Ibadan, Jihar Oyo.

Kakakin DSS, Peter Afunanya ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron ’yan jarida ranar Alhamis inda ya ce samamen ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu cewa an jibge makamai a gidan.

Afunanya ya ce, “Da zuwan jami’an tsaron, sai aka fara musayar wuta da yaran Igbohon su tara, wadanda muke kyautata zaton masu gadinsa ne. Shida daga cikinsu suna dauke da bindiga kirar AK47, ragowar ukun kuma suna amfani da mai jigida.

“A musayar wutar aka kashe biyu daga cikin yaran na Igboho, yayin da ragowar kuma suka shiga hannu.

“Jami’in tsaro daya ne suka sami nasarar harbi, kuma a sakamakon haka ya sami rauni a hannunsa na dama. Sai dai yana ci gaba da samun kulawar lafiya kuma yana murmurewa.

“Duk da cewa ba mu sami nasarar kama Sunday Igboho a gidan ba sakamakon cika wandonsa da ya yi da iska, muna son mu tunatar da shi cewa ba zai iya guje mana ba har illa Masha Allah.

“Don haka muna ba shi shawara ya gaggauta mika kansa ga ofishin jami’an tsaron mafi kusa,” inji Afunanya.

DSS ta kuma ce makaman da aka samu a gidan dai sun hada da bindiga kirar AK47 guda bakwai, jigidar harsasai guda uku, manyan bindigogin AK 47 cike da albarusai guda 30, albarusai guda 5,000, adduna biyar da kuma wukake guda biyu.

Sauran kayan sun hada da kananan bindigogi kirar Pistol guda biyu da wata lalita dauke da Dalar Amurka biyar da dai sauran tarkace.

Ya kuma ce ban da kayan da aka samu a gidan, an kuma kama mutum 13 da ake zargi, ciki har da wata mace, kuma tuni an tusa keyarsu zuwa Abuja.

A ’yan watannin da suka gabata dai Sunday Igboho ya yi kaurin suna wajen kai hari kan ’yan Arewacin Najeriya mazauna yankin Kudu maso Yamma, a fafutukarsa ta ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Oduduwa.

Ya jagoranci kone rugagen Fulani da dama a yankin tare da umartar dukkan ’yan kabilar da su bar yankin gaba daya.

%d bloggers like this: