Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta ce za ta binciki zargin da ake yi wa jami’anta na cin zarafin wani dan jaridar da ke aiki da kamfanin Vanguard, Gbemiga Olamikan.
Rahotanni sun ce Olamikan ya gamu da fushin jami’an DSS ne a lokacin da ya je daukar rahoton yaran Sunday Igboho, wadanda hukumar ta gurfanar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin.
Bidiyon cin zarafin dan jaridar ya karade kafafen sada zumunta, inda ya haifar da caccaka ga Gwamnatin Tarayya.
Da yake jawabi a kan lamarin a daren Laraba, kakakin DSS, Peter Afunanya, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa hukumar za ta binciki lamarin tare da yin adalci.
Ya jaddada cewa ’yan jarida da jami’ansu abokan aiki ne da ya kamata su yi aiki kafada da kafada domin kawo cigaban kasa.
“DSS na da alhakin samar da tsaro amma ba ta cin zarafin ’yan jarida ba. Muna da kyakkyawar alakar aiki da dukkannin ’yan jarida saboda abokan aiki ne wajen gina kasa.
“Ya kamata a fahimce su ta hanyar zaman lafiya da jituwa. Saboda haka hukumarmu za ta binciki zargin da aka gabatar,” inji Afunanya.