✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Drogba ya tallafa wa yara dubu 5 a Kwaddebuwa

Shahararren dan kwallon Chelsea da ke Ingila kuma dan asalin Kwaddebuwa Didier Drogba ya raba wa yara ’yan makaranta mazauna kasar su kimanin dubu 5…

Shahararren dan kwallon Chelsea da ke Ingila kuma dan asalin Kwaddebuwa Didier Drogba ya raba wa yara ’yan makaranta mazauna kasar su kimanin dubu 5 kayayyakin karatu da rubutu kyauta a matsayin gudunmawa don cigaba da karfafa musu gwiwar yin karatu ba tare da matsala ba.

dan kwallon ya tallafa wa yaran ne musamman marasa galihu don ganin sun samu sukunin karatu ba tare da matsala ba.
Da ma kasar ta shaidi Drogba da tallafa mata a bangarori da dama.
Ko a shekarar 2012 sai da dan kwallon ya gina wani kafataren asibiti don kwantar da marasa lafiya da aka kiyasta kudinsa a kan Fam miliyan 3 kwatankwacin Naira miliyan 750.
Kamar yada kafar sadarwa ta Supersports.com ta kalato, kayayyakin da dan kwallon ya raba ga ’yan makarantar sun hada da takardun karatu (tedt books) da jakunkuna da takardun rubutu da na koyon lissafi da ruwan sha na kwalabe da kuma kayayyakin ziyartar ban daki.