✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DPO ya yi fatali da cin hancin N1m daga hannun dan ta’adda

DPO din garin Tafa ne ya jagoranci tawagar jami’ansa wajen kama dan ta’addan mai suna Bello Muhammad.

Wani Baturen ’yan sanda da ke kula da shiyar Tafa a Jihar Kaduna, ya yi fatali da tayin cin hanci na naira miliyan daya daga hannun wani dan ta’adda da ya kama.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, kakakin rundunar ‘yan sanda jihar, Manir Hassan ya ce, an yi kamen ne a otel din Easyway da ke Tafa a ranar 19 ga watan Janairun da muke ciki ne.

Ya ce DPO din garin Tafa ne ya jagoranci tawagar jami’ansa wajen kama dan ta’addan mai suna Bello Muhammad da ya fito daga Zamfara a wani otel da ke garin, inda suka same shi da kudin da ya kai naira miliyan biyu da dubu dari uku da hamsin da ake zargin kudin fansa ne daga garkuwa da mutane.

Hassan ya ce yayin bincike, Muhammad mai shekaru 28 ya amsa cewar shi mai garkuwa da mutane ne da ke gudanar da ayyukansa a dajin Kagarko da ke Jihar Kaduna, kuma kudin da ke tare da shi wani kaso ne daga cikin kudin fansar da suka karba.

Jami’in ya ce a cikin wayarsa an gano hotunansa dauke da bindiga kirar AK47 wanda ‘yan sandan suka kwace, abinda ya sa ya yi tayín ba da naira miliyan guda ga DPOn domin kubutar da kansa, amma baturen ‘yan sandan ya ki.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kaduna, A. D. Ali ya jinjina wa DPO’n da jami’ansa saboda wannan kokari tare da kiran su jajirce wajen kara kaimi a ayyukansu.

Kwamishinan ya kuma umurci masu kula da otal-otal, da sauran wuraren shakatawa a jihar da su rika sanya ido a kan kwastomominsu a kodayaushe domin kaucewa samar wa masu aikata laifuka mafaka.