✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

DPO ya lashe musabakar Alkur’anin ’yan sanda ta farko a Kano

Rundunar ta ce ta shirya gasar ne don kyautata alakar jami'anta da jama'a.

A karon a farko a Jihar Kano, Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta shirya musabakar Alkur’ani mai girma a tsakanin jami’anta, inda Baturen ’Yan Sanda (DPO) na Karamar Hukumar Takai, SP Mahi Ahmad ya zama zakara a ajin izu 60.

An shirya gasar ne a matakin izu 60 da 40 da 20 da 10 da biyar da kuma izu biyu.

A cewar Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, an shirya gasar ce, wacce ta gudana a hedkwatar hukumar da ke Bompai, don a inganta alaka tsakanin ’yan sanda da sauran al’umma.

Ya ce an bayar da kyaututtuka kamar su tibi kirar Plasma da na’urorin sanyaya kayayyaki, da fankoki da kekunan hawa da shaddoji da kwafin Alkur’ani da kuma kudade, don karfafa gwiwar dukkan wadanda suka shigeta.

An fara gudanar da gasar ne ranar Laraba sannan aka kammala ta ranar Alhamis, kuma jimlar jami’ai 39 ne suka fafata a cikinta.

Sauran wadanda suka zama zakaru a gasar sun hada da Salihu Umar, da ya fito daga Kwalejin horar da jami’an ’Yan Sanda da ke Wudil a Jihar ta Kano (POLAC), wanda ya zama zakara a izu 40, sai Kadet Alhassan Musa a izu 20 shi ma daga POLAC.

Sauran sun hada da Kadet Hafiz A. Gama daga POLAC wanda ya zama zakara a izu 10, Sajan Sani Mustapha daga hedkwatar runduna ta daya a izu biyar, yayin da Insfekta Abubakar Mohammed shi ma daga rundunar ta daya ya zama zakara a ajin izu biyu.

Malamai da dama ne daga Jihar suka albarkaci musabakar, cikinsu har da Sheikh Ibrahim Khalil da Sheikh Abdulwahab Abdallah.

Rundunar dai ta sha alwashin ci gaba da shirya musabakar a shekaru masu zuwa.