✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dorinar ruwa: Dabbar da ke iya rike numfashi tsawon minti 5 a cikin ruwa

Aminiya ta yi nazari kan irin baiwar da Allah ya ba wannan halittar

Dorinar ruwa na daga cikin dabbobin da ke son zama a cikin ruwa, duk da dai galibin rayuwarta a tudu take yi.

Tana daya daga cikin manyan namun daji wadda galibin abincinta, ciyayi da ganyayyaki ne. Galibi, an fi samun ta ne a dazukan Afirka.

Ga wasu muhimman abubuwa game da wannan dabbar kamar yadda masana suka tattaro:

* Dorinar ruwa ita ce dabba ta uku mafi girma a doron kasa, bayan giwa da gwanki.

* Dorinar ruwa nau’i biyu ce; akwai wacce ta fi shahara da kuma girma, akwai kuma wacce take karama. Ita wadda ta fi shaharar, tsayinta kan kai kafa 16 bayan ta girma.

* Dabba ce da ta kware a ninkaya. Tana iya rike numfashinta na tsawon minti biyar a cikin ruwa.

* Masana kimiyyar dabbobi sun ce, Dorinar ruwa dabba ce mai keta. Sun ce ketarta ta samo asali ne daga matsin da mutane kan yi mata a mazauninta, kamar farmakin mafarauta da na masu kama dabbobi suna killacewa a wurare na musamman.

* Dabba ce mai cin ciyawa da ganyayyaki gwargwado. A yini, takan ci ciyawa mai tarin yawa.

* Takan dauki ciki na tsawon kwana 243, kwatankwacin wata takwas. Sannan nauyin jinjirin Dorinar ruwa sabon haihuwa, na kai maki 30 zuwa 50 a ma’aunin ‘pound’.

* Sun fi samun karsashi da kuzari a lokutan dare, sukan bar cikin ruwa inda suke hutawa zuwa tudu don kiwo da sauran bukatunsu, kana idan gari ya waye su koma ruwa.

Dorina
Dorinar Ruwa

* Suna da fikirar iya gane abokan huldarsu a tsakanin makiya daga nesa ta hanyar shakar warin jikin juna ko warin kashinsu.

* A cewar masana, ba domin yanayi ba, a zahiri ba a lissafa Dorinar ruwa daga jerin dabbobi masu fushi da keta. Amma matsin da sukan fuskanta daga wajen bil Adama ya sa suka sauya.