Ba zan boye maku ba, ni an yi mini aure ban wani iya girki ba, kuma ba na ma son shiga kicin.
Ni ba mai son girki ba ce, musamman irin girkin nan da za a tsaya tsara shi da bin dokoki da ka’idoji don dai kawai ya fito da wani dandano, launi ko tsari na musamman.
Abin da za a markade shi ya zama kashi, to mene ne na bata lokaci da ba shi muhimmanci, shi ya sa na fiye son abincin da ba sai an dafa ba irin su kayan marmari da ganyayyaki.
Allah Ya kyautata min rayuwata da ba ni miji na gani da fada abin takama da tinkaho.
Ina tsananin son sa da son kyautata masa.
Bayan aurenmu na gano cewa surukata mace da muka yi hannnun riga da ita ta bangaren girki.
Tana daya daga cikin matan da kaso mai girma na lokacinsu ya kare a kicin, tana son ciyar da sababbin nau’o’in abinci daga lokaci zuwa lokaci ta hanyar yin girki iri-iri tun daga irin namu na gida, na Larabawa, abincin Turawa, Indiyawa da sauransu.
Kayan tande-tande da makulashe kuwa ba a magana. Ta yi fice wajen iya abinci masu dadin gaske.
Maigida da sauran dangin miji na yawan yabon girkinta, kuma duk suna cewa ba su taba cin abincin da ya kai dadin nata ba.
Zuciyata ta cika da fargaba, yaya za a yi in taba iya burge maigida da girkina bayan ya tashi yana cin irin wadannan dadadan girke-girke?
Na san abin da na iya a bangaren kicin ko kama dan yatsar nata bai yi ba balle kafa.
Amma duk da haka na zauna na na yi wa kaina magana: ‘Na ce zan yi bakin kokarina sauran al’amarin kuma in danka shi ga Allah.’
Kafin nan na sanar da maigida cewa ni fa ban wani kware a girki ba, don kada ya ga abin ya zo masa daga sama.
Sai ya ce da ni “Ki kwantar da hankalinki, ni ma na fi son abinci mai sauki ba dole sai kin wahalar da kanki wajen tsara mani abinci na musamman ba.”
Jin haka ya kara kwantar min da hankali. A ranar farko da na shiga kicin dina don yin girki, na roki Allah Ya taimake ni kan haka, Ya sa girkina kada ya yi kasa da na surukata wajen dadi da tsaruwa.
Na sakankance cikin addu’a kuma na mika dukkan al’amarina ga Allah Madaukaki. Na dogara gare Shi, sai na roke Shi cewa abincina ba zai zama kasa da na surukata ba.
A lokacin na tuno da nasihar da wata malama ta yi mana inda take cewa mafi yawan mata lokutansu na karewa a kicin inda suke shirya dadadan abincin buda-baki wanda hakan ya sa ba su samun isashen lokacin yin ibada.
Ta gargadi mata da kada su yi sanya wajen ibada da yawan ambaton Allah. Domin watan Ramadan kamar wani kamshi ne mai dadin shaka kuma mai saurin bacewa.
“Don haka me zai hana ba za ku rika yin zikiri ba yayin da kuke dafa abinci?
Shin a cikinku akwai wanda take yin girki alhali tana tasbihi?
Wannan ya sa na ji son in rika yin haka, ba don in yi amfani da damar watan Ramadan ba domin muna cikin wani watane daban, sai don fatar Allah Ya sa abincina ya yi dadi! Wannan ya sa na kudiri aniyar yin Bismillah a kowane mataki na girkina.
Daga nan kuma sai na ga ai bayan Bismillah, me zai hana in rika karanta Suratul Ikhlas a kowane mataki na girkina, domin ina tsananin son wannan Surah ga shi kuma tana da saukin karantawa kuma akwai lada mai yawa ga karanta ta!
Cikin taimakon Allah sai na ci gaba da yin haka, kuma Allah Ya ba ni iko ina yin tasbihi da tahmidi a lokacin da nake dafa abinci da kuma lokacin wanke kwanoni da tsaftace kicin.
Na lura maigida kullum yana yawan yaba abincina har ma yakan ce girkina ya fi na mahaifiyarsa dadi.
Amma ban yarda da zancensa ba, na dauka giyar angwanci ne ke dibarsa yake yaba min fiye da kima.
Amma da na lura yana yawan maimaita yabon girkin nawa, sai na ce kila girkin nawa da dan damarsa.
Musamman da na fahimci ashe shi mutum ne mai son a tsara girki ta kowane fanni, ba kamar yadda ya fada min shi mai son abinci mai saukin girki ba ne, ya fadi haka ne kawai don ya karfafa min gwiwa.
Wani zuwa da surukata ta yi ta kwana a gidanmu, ita ma ta yi ta yaba dadi, dandano da tsarin girkina. Sai na dauka kawai tana min kara ne.
Amma sai na lura duk in ina kicin biyo ni take yi ta ja ni da hira amma idonta yana kan abin da nake yi, ko na ce ta je ta huta, ba za ta tafi ba, sai ta yi ta yi min tambayoyi kan salon girkin da nake yi.
Ban gane dalilin da ya sa haka ba sai bayan ta koma gidanta sai ta bugo min waya ta ce na hada ki da Allah ki sanar da ni sirrin dandanon abincinki, domin duk na bi yadda na ga kina yi amma dandanon ba irin naki ba ne.”
Sai na ce “Umma ko dai tsokanata kike?”
Amma ta rantse min ba wasa take ba! Wannan abin ya ba ni mamaki sai na fara zurfafa tunani domin in gano dalili, amma ban samu komai ba sai zikiri da karatun Suratul Ikhlas da tasbihi a wasu lokutan sai na ce mata: “Umma in gaya maki gaskiya?”
Ta ce “Eh.” Sai na ce mata kin ji, kin ji, yadda nake yi. Ta yi mamaki matuka amma kamar ba ta gasgata ba.
“A karo na gaba da ta ziyarce mu sai na lura ta kara sa min ido sosai don ta tabbatar da maganata.
“Bayan ta koma gida sai ta bugo min tana cewa ta fara yin yadda ni ma nake yi kuma ta fara lura da ci gaba a cikin dandanon abincin.
“Abin da yake ba ni al’ajabi da sa ni murmushi game da wannan al’amari shi ne, yanzu ba na kin girki ko bata lokaci a kicin ina tsara abinci.
“Musamman in na kunna kira’ar Kur’ani ina saurare ko wa’azzuka daga mabambantan malamanmu.
“Wannan ya sa lokacin girki ya zama lokacin nishadin ruhi a gare ni, har ba na lura da wucewar lokaci har sai na gama komai kuma ba na jin wucewar lokaci sai na gama da komai.
“Yanzu duk wasu kayan makulashe da tandetande ina bata lokacina in zauna in tsara in dafa ko in gasa.
“Duk wanda ya san ni cikin abokai da ’yan uwa suna mamakin wannan canji nawa, da yawa ba su yarda sai sun gani da idonsu.
Dukkan godiya, jinjina daukaka da kambamawa sun tabbata ga Allah Madaukaki wanda Ya sanya sirruka a cikin ambatonSa da ba mu san yawa ko iyakarsu ba.