✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Don uwargida: Ladubban tarbar kishiya

Ba mai yaye maki bakin cikin da zuwan kishiya ya kawo maki, sai Sarkin Rahma Allah.

Assalamu alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

A ci gaba da amsa tambayar da ta gabata wancan makon, ga bayani kan ladubban da ya kamata uwargida ta bi yayin karin auren maigidanta.

Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya zan ya amfanar da su, amin.

Ladabi na 1: Kulla niyyar alheri: A lokacin da uwargida ta samu labarin bukatar maigidanta ta karin aure, a wannan lokaci tunani barkatai za su watsu cikin zuciyarta na abin da za ta yi game da wannan al’amari da ya samu rayuwarta.

Cikin irin wadannan tunane-tunane, tabbas Shaidan zai zuro nasa.

Sai in an yi dace mace mai tsananin tsayar da addini ce, hakan zai hana tunanin da Shaidan ya zuro yin tasiri.

To a irin wannan lokaci ne uwargida sai ta kulla niyyar alheri ta wadannan hanyoyi:

• Ta yi niyyar cewa ba za ta bari ko da wasa ba ne, wani abu daga cikin wannan al’amari ya nesanta ta da Ubangijinta; kuma za ta yi iya kokarinta ta ga ba ta saba wa dokokin Allah Madaukakin Sarki ba, ta ga cewa a karshe wannan al’amari ya kara kusantar da ita da Ubangijinta ba nesanta ta ba.

• Sannan ta yi niyyar za ta yi iya yin ta wajen karin kyautatawa da ladabi ga mijinta da kokarin kauce wa saba masa ta kowace fuska, har Allah Ya sa a yi wannan abu a kare lafiya.

• Kuma ta yi niyyar za ta yi iya kokarinta wajen gani cewa wannan al’amari bai zubar mata da mutunci ko daraja ba a wajen mijinta, cikin danginta, makwabta, ’yan uwa da kawaye.

Musamman in ta yi la’akari da yadda zafin kishi ke sa wadansu mata su zama kamar zararru, duk inda suka zauna suna zagin abokiyar zamansu suna bakanta ta, ba sa la’akari da cewa kansu suke rage wa daraja da yin haka.

• Sannan uwargida ta yi niyyar yin zaman lafiya da abokiyar zamanta, kyautata mata da ba ta duk wani hakkin da ya kamata mutum ya bai wa dan uwansa Musulmi.

• Ta yi niyyar dannewa da boye kishinta ta yadda ba zai kai ta ga aikata wasu abubuwa da wata rana za ta yi da-na-saninsu ba.

Ladabi na 2: Kara kusantar Ubangiji (SWT) Wannan lokaci ne mai zafi da kuncin rai, yanayi ne mai cike da bacin rai, halin kakani-ka-yi da neman mafita ga mafi yawan mata.

Ya ’yar uwa uwargida! Kada ki yi dubi zuwa ga wadansu kawaye ko ’yan uwa da nufin su share maki hawaye domin wallahi ba za su iya ba, saboda komai irin yadda ki kai kokarin sanar da su halin da kike ciki ba za su iya fahimta ba.

Ki koma ga wanda Shi kadai Ya san hakikanin abin da ke cikin zuciyarki.

Shi kadai Ya san irin tsananin zafin kishinki da yadda yake ci maki zuciya, Shi kadai zai iya share maki hawaye, kawaye da ’yan uwa sai dai a ba ki shawarwari na bogi, wadansu su ba ki shawarar irin kayan da’ar da ya kamata ki hada, wadansu su taimaka maki da irin canjin da za ki yi wa kayan adon gidanki, wadansu su cika ki da irin yadda za ki musguna wa abokiyar zamanki in ta zo, wadansu su ja ki ga bokaye da ’yan tsibbu, amma duk ba mai iya cire maki wannan zafin tafarfasar kishin da kike ji.

Ba mai yaye maki bakin cikin da zuwan kishiya ya kawo maki, sai Sarkin Rahma Allah Madaukakin Sarki! Wallahi in kika dulmiyar da kanki cikin ibada da kara kusantar Allah, sai ki nemi zafin kishin nan ki rasa, sai ki ji wata irin natsuwa ta lullube ki marar misaltuwa.

Amma abin takaici shi ne da yawa matan Hausawa kishiya ce sanadiyyar bacewarsu daga kyakykyawar hanyar Allah Madaukaki, Kishiya ke kai su ga aikata babban sabon da ba su taba zaton za su iya aikatawa ba a rayuwarsu, kishiya ke sa su sayar da imaninsu wajen yin shirka da Allah wurin ’yan tsibbu da bokaye.

Duk uwargidan da ta bari kishiya ta yi sanadiyyar raba ta da wani bangare na imaninta, to, lallai wannan kishiya ta sha da ita da yawa.

Zan dakata a nan, sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.