✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake ‘Spring rolls’

Bayan abincin buɗe baki, uwargida za ta iya koyan wannan girki a matsayin sana’a da za ta iya kawo mata kuɗi.

Assalamu alaikum uwargida tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya.

Kamar yadda a kullum nake ba da shawarar cewa, yana da kyau uwargida ta ƙware wajen girke-girke, wato yana da matukar muhimmanci ta ƙware wajen girkin gargajiya da na zamani da kuma na ƙasashen waje.

Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake ‘spring roll’.

Bayan abincin buɗe baki, uwargida za ta iya koyan wannan girki a matsayin sana’a da za ta iya kawo mata kuɗi.

Abubuwan da ake bukata: · Karas · Albasa · Attaruhu · Tafarnuwa · Kabeji · Kayan dandano · Koren tattasai · Kori · Man gyada · filawa

Yadda ake yin hadin:

A sami kwano sannan a zuba garin filawa da ruwa ya dan yi tsororo. Sannan a sami tukunya a zuba man gyada kadan sannan ana zubawa ana kwashe wa.

Za a ga ya yi lafelafe. Bayan an gama da ƙullun sai a ajiye su a gefe.

A kankare karas a yayyanka shi kananan tare da kabeji a wanke a ajiye a gefe. Bayan haka, sai a jajjaga tafarnuwa da attaruhu.

A yayyanka albasa da koren tattasai a dora tukunya sannan a zuba karas da jajjagen attaruhu da yankakken kabeji da albasa a yi ta gauraya su.

Sannan a dauko magi da kori a zuba har sai ya dan nuna sannan a sauke a bari ya huce.

Bayan ya huce sannan sai a dauko wannan wainar filawar da aka ajiye sai a rika diba cokali biyu na hadin a zuba a kai sannan a yi masa nadin tabarma a kalmashe bakin sannan a sake dora man gyada a wuta a soya har sai ya soyu sannan a sauke.