Aminiya: Hajiya ki gabatar da kanki?
Bilkisu Hadejia: Sunana Hajiya Bilkisu Shehu Hadejia, amma an fi sanina da Hajiya Goggo Hadejia, ni daya ce daga cikin ‘ya’yan Alhaji Shehu Mujaddadi. An haife ni a garin Hadejia a shekarar 1966, kuma na yi makarantar furamare a gida Hadejiya kuma na jima ina tunanin kafa makarantar Boko tun ina karama da nufin taimakawa marasa karfi musamman mata.
Aminiya: Yaushe ne kika fara tunanin kafa makaranta?
Bilkisu Hadejia: Na fara tunanin kafa makaranta tun a shekarar 2008 amma burina ya fara cika ne a shekarar 2010 a lokacin zamanin gwamnatin Sule Lamido, inda gwamnatin tasa ta bani fili kyauta saboda gori da wasu mutane suke wa Jahar Jigawa cewar jaharmu babu makarantu na zamani, a lokacin har ana ce mana ba mu da gidaje, shi ne sai nake ce masu ai a sama suke kwana tun da ba su da gidaje.
Da Lamido ya zama gwamna a Jahar Jigawa ne ni ma na yunkura na sami karfin gwiwa na fara yin makaranta saboda ya samar da gidajen dan masara karfi kuma ya gina asibitin Rashid, saboda duk wanda zai yi hijira ba komai yake tunani ba, sai ina zai kai iyalansa? In ba su da lafiya kuma ina zai kai su jinya? Idan ya je bakon waje, amma a ganin Lamido ya fara samar da gidajen ma’aikata da babban asibitin kwanciya na Rashid, shike nan sai hakan ya bani kwarin gwiwa na gina makarantata ba tare da tunanin wata matsala ba.
Aminaya: Mene ne dalilin sanya wa wannan makarantar taki suna Standard?
Bilkisu Hadejia: Na sanya wa makaranta ta suna Standard ne saboda an yi mana gorin cewar ba mu da ‘Standard School’ shi ne ya sa na sanya wa tawa suna ‘Dutse Standard School’ kuma na gode wa Mai Martaba Sarkin Dutse da Baba Galadiman Dutse domin duk abin da na zama a harkar koyarwa da taimakonsu makarantar nan ta samu kafuwa a nan Dutse. Haka zalika ba zan taba mantawa da ubana ba tsohon dan takarar gwamnan Jahar Jigawa, Alhaji Aminu Ringim saboda shi ne ya kara min karfin gwiwa wajen ganin makarantar nan ta samu kafuwa a Jahar Jigawa ga shi yanzu makarantar nan ta zama abar alfahari a fadin Najeriya, domin wallahi yanzu duk Najeriya babu inda labarin makarantar Dutse Standard bai kai ba.
Kuma na gina ita wannan makarantar ne da nufin in taimaka wa ‘ya’yan marasa galihu su samu ilimi mai nagarta, kuma in taimaka wa ‘ya’yan ma’aikata da suka samu kansu a cikin halin sauyin wurin aiki, saboda sau da yawa in aka yi wa ma’aikata sauyin wurin aiki ba sa zuwa da ‘ya’yansu saboda rashin wadatattun wurin da ‘ya’yansu za su samu ilimi mai nagarta. A lokacin da na shigo birnin Dutse ban san kowa ba, shi ne na fara zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammed Sunusi a matsayinsa na uban kasa domin shi ne uban kowa, don neman albarka da neman goyan bayan masarauta. Kuma na fara makarantar ne a wani gidan haya a unguwar Yalwawa da ke garin Dutse da na fara da daukar dalibai ‘yan aji daya da daliban nazire, inda na fara da yara 57 da kuma malamai bakwai.
A lokacin kasancewar ni bakuwa ce ba na so in debi daliban da yawa domin gudun kada a samu matsala, domin tafiyar da dan adam al’amari ne mai wahalar gaske, dole sai an natsu sosai. Bayan shekara biyu shi ne na sake tunani na dauki sabbin dalibai da kara yawan malamai, inda ta kai na dauki dalibai 187 da malamai 12, bayan shekara biyu a lokacin da makarantar ta kai aji uku, shi ne na sauya wuri na kama wani gida haya a bakin titin Yalwawa a lokacin da dalibai suka kai 280.
Aminiya: To a wane lokaci ne kika gina wannan makaranta da kike da burin ginawa a Jigawa ta zama ta tsaya da kafarta?
Bilkisu Hadejia: Yanzu na kammala gina makarantar anan garin Dutse saura ‘yan gyare-gyare kalilan ya rage min a makarantar, yanzu na gina makarantar ina da dalibai sama da 500 da kuma malamai sama da 26, sannan gaba daya ina da ma’aikata mutum 41 a wannan makaranta.
Kuma na fara tunanin kafa ita wannan makarantar ce tun a shekarar 1988 lokacin da ake min gori saboda haka ne ma na dawo gida Jahar Jigawa domin ni ma in bada tawa gudunmawar domin bunkasa harkokin ilimi a Jahar Jigawa.
Aminiya: Ko zaki iya tuna irin nasarorin da kika samu daga kafuwar ita wannan makaranta zuwa yanzu?
Bilkisu Hadejia: Babbar nasara ta farko dai ita ce makarantar ta amsa sunanta na ‘Dutse Standard School’ domin makarantar ta yi suna a fadin Najeriya, kowa ya santa saboda duk wadanda ya ransu suke karatu a makarantar ba na shakkar a gwada su da kowace makaranta a fadin Najeriya, domin iyaye da dama sun bar Jahar Jigawa sun bugo waya suna yi min godiya akan yadda mu ka bai wa ‘ya’yansu karatu da tarbiyya. Kuma nagode Allah, wallahi dalibanmu sun sha bamban da sauran dalibai a fadin Najeriya saboda dalibaina suna zama jarabawa da daliban ‘Santilus Secondary School’ dake Kano kuma suna yin jarabawa da daliban ‘Bamaina Academy’ kuma kwazonsu ya fito fili kowa ya sansu.
Aminiya: Ya ya kuma batun kalubale, ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta daga kafuwar makarantar zuwa yanzu?
Bilkisu Hadejia: Agaskiya na sami matsaloli masu yawa, musamman a halin yanzu da makarantar take habaka sunanta yana dada dagawa, jama’a suna saninta, saboda a duniya babu abu mai wahala irin lura da dan adam, mu kuma muna yin bakin kokarinmu wajen lura da baiwa yara tarbiyya da kula da karatun yara, saboda iyaye amana ce suka dora mana. Matsala ta biyu kuma da yawa daga cikin iyayen yara ba sa kula da biyan kudin makaranta na yaransu, kuma mu da kudin ne muke kula da hakkin malamai da aiwatar da dukkan gyare-gyaren makaranta, kuma matsalarmu ta uku bamu da wuta, hakan ya biyo bayan karancin kudade da muke fuskanta, saboda haka maimakon ace sun hada wutar NEPA a makarantar mun dogara ne da janareta, amma muna da burin hada makarantar da wutar NEPA din anan gaba.
Aminiya: Ko ki na da wata kira da zaki yi ga iyayen yara ko shawara?
Bilkisu Hadejia: Kira na ko shawara ta ba ta wuce in ce iyayen yara su yi wa Allah su rika kula da hakkin kudin makaranta su rika biya akan lokaci, domin ba son ranmu ba ne mu rika kora yara gida a lokacin karatu, saboda gazawar iyaye wajen biyan kudin makaranta.