✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Don maslahar Kano aka dawo da Sarki Sanusi II — Gwamnati

Gwamnatin ta ce akwai waɗanda ba sa kishin jihar da ke son tada zaune-tsaye.

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta dawo da Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ne, domin masalahar jihar.

Hakan na zuwa ne bayan da aka shiga ruɗani a jihar, inda sarakuna biyu, ke iƙirarin mulkin masarautar Kano.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Baba Halilu Dantiye, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce gwamnatin jihar ta nuna damuwa kan rahotannin da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai.

Kwamishinan, ya ce sun gano yadda wasu kafafen yaɗa labarai marasa kishi ke amfani da batun rushe masarautu huɗu da majalisar dokokin jihar ta yi, wajen haddasa fitina.

Sanarwar ta ce, “Duba da halin da jihar ke ciki a halin yanzu, gwamnati ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma kuma komai na tafiya daidai.

“Saɓanin rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa, babu wata zanga-zanga da ta faru a Jihar Kano. Gwamnati na sane da abubuwan da ke faruwa, an samu wasu marasa kishi sun ɗauko hayar yara da ’yan daba wanda hakan bai shafi abin da ke faruwa ba.

“Waɗannan marasa kishin da aka ɗauko haya, ba su da burin komai face tada zaune-tsaye. Al’ummar Jihar Kano sun ƙi biye musu, inda suka fahimci haƙiƙanin matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka.

“Kazalika muna tabbatar da matakin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ɗauka na rushe masarautun bisa doka tare da dawo da Sarkin Kano na 14 domin masalahar jihar. Da yawan jama’a sun yi maraba da wannan mataki da gwamnati ta ɗauka saboda sun fahimci alfanun hakan.”

Gwamnatin ta ce wasu ‘yan siyasa na amfani da yanayin da ake ciki domin haifar da tarzoma, yayin da ta ce wasu na amfani da kafafen yaɗa labarai wajen yaɗa labaran ƙarya.

“Abubuwan da suke yi ba ya wakiltar haƙiƙanin ‘yan Kano face son rai da cimma muguwar buƙatarsu.

“Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano. Gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta ba, na ɗaukar dukkanin matakan da suka dace na wanzar da doka da oda tare da kare haƙƙin ‘yan Kano,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta buƙaci jama’a da su yi watsi da rahotannin kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa tare da yin kira ga kafafen da su kasance masu yin aikin jarida bisa doka da tsari, sannan su kasance masu fayyace gaskiya.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf na ci gaba da jajircewa wajen samar da ci gaba a jihar tare da yin kira ga al’ummar jihar da su bai wa gwamnatin haɗin kai.”