✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Don magidanta: Darasi da labari

Maigidan da ya yi wa matansa biyu wayo! Daga labaran magabata...

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa amin

Maigidan da ya yi wa matansa biyu wayo! Daga labaran magabata, wani mutum daga kabilar Banu Nawfal ya kara aure.

Matar ta biyu ta kasance kyakkyawa mai kyan zubi. Matarsa ta farko mai suna Ummu Mahjan ta kasance mai duhun fata, sai ta shiga damuwa bayan jin labarin auren mijinta.

Kishi ya turnuke ta har ta je ta samu mijinta tana tuhumarsa. Amma sai ya yi mata bayani kamar haka: “Ina rantsuwa da Allah Ummu Mahjan ba ki bukatar ki tuhume ni cikin kishi. Ni tsoho ne, ke ma tsohuwa ce, ba dalilin da zan tuhume ki.

Ba wanda ya kai ki daraja a idona kuma ba wanda zai kai ki more rayuwa da ni. Don haka ina shawartarki da ki aminta da kudirina kuma ki guji sauraron saken-saken zuci.

Wannan bayani sai ya kwantar mata da zuciya ta samu natsuwa. Bayan ’yan kwanaki kadan, sai ya ce da ita, shin ba za ki so ki zauna gida daya tare da amarya ba? Ina sa ran hakan zai kara maku dankon zumunta da kuma zaman lafiya a tsakaninku kuma hakan zai kara hada kanmu kuma ya hana wasu daga waje tsoma baki cikin harkokin gidanmu.

Sai ta amince da haka, sai ya ba ta Dinari daya tare da ce mata: ba na son abokiyar zaman ta rika neman takara da ke don kawai ta ga kina more wasu abubuwan, don haka ga wannan dinarin ki tanadar mata wata kyauta ta musamman a lokacin haduwarku.

Sai kuma ya je ga amaryasa ya ce da ita, na yi niyyar in hada ki zama waje daya da Ummu Mahjan, tana son ta karrama ki amma ba na son ta rika takara da ke saboda kawai ta ga kin fi ta more wasu abubuwa, ga wannan Dinarin ki tanadar mata wata kyauta ta musamman don kada ta samu kokwanto a zuciyarta game da ke. Amma kada ki sake ki sanar da ita cewa ni na ba ki Dinaren.

Sannan sai ya je ya samu amintaccen abokinsa ya ce da shi, na shirya hada amaryata tare da Ummu Mahjan gobe, ina son ka ziyarce mu lokacin karin kumallon safe, ni kuma zan gayyace ka ka karya kumallon tare da mu.

Bayan mun kammala sai ka tambaye ni wacce na fi so daga cikinsu? Zan bayyana bacin raina a kan tambayar amma sai ka dage kai lallai sai na amsa maka. Washegari da safe amarya ta ziyarci Ummu Mahjan kuma abokin nasa shi ma ya je kamar yadda suka tsara.

Bayan sun gama karyawa sai abokin ya juya ya dube shi ya ce “wacce ka fi so daga cikin matan nan naka biyu?” Sai maigidan ya ce “Subhanaallah! Yaya kake irin wannan tambaya bayan su duka matan suna jin ka? Lallai wannan tambaya ba ta dace ba!” Amma abokin nasa ya nace sai ya amsa masa, sai ya ce “ina son wacce aka ba Dinari daya, ba zan kara wani abu ba a kan wannan kalami.” Kowace daga cikin matan ta yi murmushin jin dadi, tana tunanin ita ake nufi.

Hikimar da ke cikin wannan labari shi ne duk wani magidanci da ya kasance yana da mata sama da daya, to sai ya hada da wayo, dabaru da hikimomi, mafi yawa lokuta da karya daya biyu nan da can wajen tafiyar da su don samar tabbataccen zaman lafiya da amintar juna cikin zamantakewar iyalansa gaba daya.

Kuma dole sai da taka-tsantsan wajen aikata irin wadannan dabaru na zamantakewa.

Misali, duk ranar da tsautsayi ya sa daya daga cikin matan wannan magidanci suka gano cewa ga abin da ya yi ka san akwai gumurzu kuma duk wani kalami da zai gaya masu nan gaba ba za su kara yarda da shi ba.

Wata daga cikin masu karatu ta taba ba ni labarin yadda mijinta yake yawan aiko mata sakonnin soyayya ta waya musamman lokacin da ya yi tafiya, ya rika nuna mata ita ce mowa ba matar da kai ta wajensa da sauran irin wadannan kalamai, ta yi ta jin dadi a zuciyarta, har tafiyar takama take tana yi wa kishiyarta kallon banza a matsayinta na bora wacce miji bai so.

Ta ce sai wata rana ta ari wayar kishiyarta za ta yi wani abu, daga nan ta wuce ta yi mata leken asiri, kawai sai ta ga irin sakonnin soyayyar da yake turo mata irinsu sak yake tura wa kishiyarta ba bambancin ko da harafi daya.

Ta ce tun daga ranar komai ya ce ta wannan fannin ganin take ya tura wa dayar. Da fatan magidanta za aikata haka tare da la’akari da kuma taka-tsantsan.

Sai makon gobe in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.