✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labaran Auratayya: Wani hanin ga Allah baiwa ne!

Tabbas, wani hanin ga Allah baiwa ne

Labarin salihar kishiya

Kauye daya muka tashi da maigidana. Babansa ne limamin kauyenmu, babana ne na’ibinsa. Layi daya muka tashi, shi ne babban abokin yayana, ni ma kanwarsa ita ce babbar aminiyata.

Bayan ya yi sauka ya dawo daga makarantar allo, sai ya sa kansa makarantar boko a babban garin kauyenmu. Saboda hazakarsa da kuma yawan shekaru, aka tsallakar da shi ya gama karatun cikin shekaru hudu.

Kafin ya tafi sakandire, iyayenmu suka shawarta tsakaninsu suka hada mu aure. Ina kauye har ya gama karatunsa a makarantar horar da ma’aikata.

Daga nan ya samu aiki a babban birnin jiharmu. Bayan ya samu gida ya zo ya dauke ni, muka koma birni da zama.

Muna haka har muka shekara bakwai da aure amma ko batan wata ban taba yi ba. Mijina bai taba yi min mitar rashin haihuwa ba ko ya nuna ya kosa in haihu. Mijina yana da kyawawan dabi’u, duk wanda ya zauna da shi sai ya ji dadin zama da shi don haka yake da abokai da yawa.

Kyawawan dabi’unsa ne ma suka sa ogansa na wajen aiki ya ba shi babbar ’yarsa aure duk kuwa da akwai wani dan babban mai kudi kuma daga cikin manyan gari da ke neman aurenta.

Yarinya ce karama sosai amma tana da hankali da sanin ya kamata. An kawo ta ko haila ba ta fara ba, ta dauke ni tamkar uwa ba kishiya ba. Komai za ta yi sai ta sanar da ni. Ba ta bari na yi aikin komai a cikin gidan.

Duk da kyawawan hali irin na maigidanmu, ranar da yake dakinta wata sa’in yakan sayo mata kayan dadi kamar balangu da kayan marmari da madara ya ba ta, ba tare da na sani ba.

Na san har da tunanin cewa ta saba cin irin wannan kayan dadi a gidansu da kuma ganin ita yarinya ce ga ta kuma amarya amma ba wai don nuna bambanci ba. Ita kuwa komai ya ba ta sai ta raba biyu ta kawo min nawa.

Shi ma da ya gane irin halinta sai ya kawo kunshi biyu kowa da nasa ko ya kawo ya ce mu raba. Ta na samun ciki ta ce ta ba ni jaririn, da ta yaye shi ya zama nawa. Amma tana haihuwa sai uban mijinmu ya hana wannan kyautar, ya ce ta rike danta. Sai a haihuwa ta biyu tana yaye yaron ya dawo dakina.

Daman tare muke renonsu da kula da su da dukkan hidima da tarbiyya. Sai yaran sun yi wayo sosai ne suke gane asalin mahaifiyarsu daga cikinmu. Yanzu haka muna tare, yaranmu duk sun girma sun kammala karatu sun yi aure.

Babban yaronmu bayan ya kai mai gidanmu Makka sai ya biya wa mahaifiyarsa, ta ce a’a, sai dai ya biya mani ko ya biya mana gaba daya mu tafi tare. Sai dai shi ya tafi, da shekara ta zagayo ya biya mana muka tafi tare.

Maigidanmu ya riga mu gidan gaskiya, muna nan zaune tare a katafaren gidan da babbar ’yarmu ta saya mana muna hidima da jikokimmu kamar yadda muka yi da yaranmu.

Allah bai ba ni haihuwa ba, amma ya ba ni salihin miji wanda ko da da rana daya bai taba nuna min na kasa ba saboda rashin haihuwa kuma bai daina nuna so da kauna gare ni ba har ya koma ga mahaliccinsa. Allah bai ba ni haihuwa ba amma ya ba ni kishiya da ta maida ni kamar shakikiyar ’yar uwa ta. Ta ba ni yaran da suke sona da mutunta ni kamar yadda suke so da mutunta mahaifiyarsu.

Kishiya wacce ba ta san ko miye kishi ba, kishiya wacce ba ta da kulli da mugun nufi a zuciyarta. Lallai wani hanin ga Allah baiwa ne. Ina godiya ga Allah da dukkan rahamominsa, musamman na salihar kishiya.

Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a ko yaushe, amin.