Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin.
Don Allah me mutum zai yi idan ba ya iya gamsar da matarsa saboda yawan shekaru?
- Ya kashe budurwarsa mai shekara 13 ya kone gawarta bayan ya yi mata ciki
- An kama dan daudun da yake zagin kabarin mahaifiyar abokin fadansa na TikTok
Fahimtar matsala rabi ne na maganin warkar da ita. Don haka kai da uwargida ku fahimci cewa kamar yadda yawan shekaru ke canja yanayin jiki, hatta tafiya da sautin murya sukan canja saboda yawan shekaru, to haka ma yawan shekaru ke canja bangaren sha’awa da ibadar aure.
Yawan shekaru na haifar da sanyin sha’awar ita kanta da sanyin gaba da saurin inzali da kuma sanyin gamsuwar ibadar aure.
Abin da a lokacin samartaka ake jin sa wuta-wuta, sai ya koma garwashi ko toka-toka saboda yawan shekaru. In ya kasance uwargida na da sauran yarinta, sai a rika samun matsala.
Don haka ya kamata ta fahimci cewa haka yanayin yawan shekaru ya zo ga maigidanta, ta sa hakuri da dangana a zuciyarta, don yawan damuwa da bayyana damuwar ba za su haifar da komai ba sai dai su kara dagula matsalar.
Musamman in ta tuna cewa akwai da yawa matan da suke auren matasa kuma suna fama da matsalar rashin samun gamsuwar. Duk da cewa yanayin dan Adam ne raguwar karfin sha’awa lokacin tsufa, akwai wasu abubuwa da suke kara assasa tasirin haka:
Yawancin abin da ke haifar da matsalolin sha’awa ga tsofaffi shi ne raunin jijiyoyin jiki duka musamman jijiyoyin al’aura. Don haka sai a dage da yawaita motsa jiki a-kai-a-kai.
Hanya mai sauki ita ce a yi tafiya a kasa ta tsawon minti 30 a kullum, sannan a rika motsa jijiyoyin al’aura, lallai wannan zai yi tasiri sosai wajen kara karfin sha’awa da rage aukuwar sanyin gaba ga tsofaffi.
Gabatowar shekaru na iya haifar da karancin sinadaran sha’awa a cikin jini, binciken likita zai bayyanar da haka, in har hakan ta tabbata akwai kwayoyin da likita zai rubuta don samun karuwar sinadaran sha’awar.
Akwai wasu cututtuka da yawan shekaru ne ke jawo su kuma sukan yi tasiri kwarai ga ma’aikatar sha’awa, musamman ciwon suga na shafar jijiyoyin al’aura. Sannan magungunan wasu cututtuka musamman hawan jini da ciwon suga suna haifar da sanyin gaba.
A irin wannan sai dai a yi aiki da umarnin likita.
Ina fama da karancin maniyyi da rashin karfin gaba, a ba ni shawara.
Abubuwan da ka iya haifar da raunin gaba da karancin maniyyi:
Yawan shekaru na cikin abubuwan da suke haifar da rashin karfin gaba da rashin ruwan maniyyi. Don haka in aka fara tara shekaru hakan ya faru, to wannan haka tsarin al’adar jikin dan Adam take.
Amma in babu yawan shekaru, to abubuwa daban-daban ke haifar da haka da suka hada da: karancin sinadaran sha’awa a cikin jini, musamman in haka na faruwa hade da wasu cututtuka kamar yawan gajiya, sanyin sha’awa da tsotsewar gaba da maraina.
Sannan ciwon suga na haifar da raunin jijiyoyin jiki kuma kan iya sa hanyar fitar maniyyi ta dode maniyyin ya koma cikin maifitsara maimakon ya fito waje.
Cutar kaba na iya haifar da karancin maniyyi da raunin gaba musamman wacce aka yi wa fida ko sakiya. Haka shan magungunan hawan jini na iya haifar da wannan matsala, don haka shawara ita ce a daure a yi wa likita bayani don wannan matsala ce da take da sabubba daban-daban a likitance.
Binciken likita ne kadai zai gano musabbabinta da samar da maganin da ya dace. Yawan cin kayan marmari da magunguna Musulunci da yawan cin kwadon ganyayyaki da kuma yawan cin farfesun kaza da na naman shanu ko tumaki da kuma romon ’yan shila na iya farfado ko kara karfin sha’awar da yawan shekaru ya sa ta lafa.
Idan lokacin sanyi ya zo gabana sai ya rika tsatstsagewa kuma da sanyin ya wuce sai ciwon ya mutu, wane irin ciwo ne wannan, sannan mene ne maganinsa?
In dai lokacin sanyi kadai hakan ke faruwa, to wannan na nuna cewa akwai matsananciyar matsalar rashin isashshiyar laima a gaba daya jiki. Yanayin hunturu kuma na tsotse duk laimar da cikin sarari da laimar fatar jikin dan Adam. Abubuwan da za su taimaka don samun saukin wannan matsala sun hada da: A riki kula da fata a koyaushe ta hanyar tsabta da shafe duk jiki da mai ba sai lokacin hunturu kadai ba.
A rika sa gyauto na maza wato dan pan ko dan diras a ciki kafin a sa wando. Wannan zai ba da karin kariya daga busarwar da hunturu ke kawowa. Yawan shan ruwa na kara yawan laima a jiki, yawan shan shayi ko naskafe na rage laimar jiki. Don haka sai a kiyaye.
Haka yawan cin kayan zaki na rage lafiyar fatar jiki wanda hakan zai yi tasiri ga karantar man da fata ke sarrafawa don hana bushewa. A guji wanka da ruwan sanyi domin hakan na busar da jiki, in ya zama dole a rika kashe zafi kadai.
Man kade na maganin bushewa da kaujen fata musamman in aka riki shafa shi kullum safe da yamma.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koyaushe, amin. (Maimaitawa)