Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Ga cigaban bayani daga inda muka kwana kan ingantattun hanyoyin da ya kamata ma’aurata su bi don samar da kyakykyawar tarbiyya ga ‘ya’yansu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Bayani Kan Shayarwa: Shayarwa tana da matukar muhimmanci ga rayuwar jariri ko mu ce ita ce gaba daya ginshiki da tabbatar da dorewar rayuwar jariri. Nonon mahaifiya na bayar da abinci mai dauke da dukkanin sinadaran gina jiki da jariri ke bukata, yana bayar da kariya ga jariri kuma ya haifar masa da natsuwar zuciya. Don haka yana da kyau uwa ta kula sosai da yin aiki da ladubban shayarwa don samar da cikakkiyar kariya da kulawa ga jaririnta.
1. Farawa da Bismillah: Kodayaushe aka dauki yaro za a shayar da shi a fara fadar Bismillah kafin a ba shi ya fara tsotsa, wannan kariya ce daga kwayoyin cuta, shaidan da dukkan wani abin ki.
2. Tsabta: Mahaifiya ta kula sosai da tsabta wajen shayarwarta, ta hanyar wanke wajen da kyau lokacin wanka, sannna bayan kowane shayarwa ta goge wajen da ta bari ya bushe kar ta rufe shi da lema wannan na iya sa kwayoyin cuta su sami yaduwa wanda kuma suna shafar lafiyar jariri. Mahaifiya ta rika suturta wajen shayarwarta kar ta bar su kodayaushe a sake kura da iska na isa garesu.
3. Riko da kyau: Watau kodayaushe Mahaifiya ta tabbatar ta yi kyakykyawan riko ga jaririnta lokacin shayarwa kuma ta saita bakinsa sosai ta yadda zai rufe dukkan wajen tsotsan, rashin yin haka na iya haifar da zafi da tsatstsagewar fata.
4. Cin abinci mai gina jiki: Gwargwadon kyawun abinci da uwa ke ci gwargwadon kyawun nonon da jikinta zai samar ga jaririnta. Don haka yana da matukar muhimmanci uwa ta rika cin abinci mai kyau mai gina jiki ta kuma guji duk wasu cimaka masu lahani.
5. In Mahaifiya ta samu matsala ga wajen shayarwarta ta yi kokarin neman magani cikin gaggawa tun kwayar cutar ta kai ga yin karfi ko ta isa ga jariri. Kuma ta daure ta cigaba da shayarwa haka komai zafi domin rashin shayarwa zai kara wa cutar tsanani.
6. In ruwan nono ya yi yawa ana iya yin famfon shi da famfon wajen shayarwa don samun sauki. In kuma ruwan nono ya yi kadan sai a dage da yawan shayar da yaro, cin abinci masu gina jiki da karin neman maganin ruwan nono a asibiti da kuma wajen masana.
Hukuncin Shayarwa a Shari’a: Shayarwa hakkin jariri ne wanda dole iyaye su samar masa da shi. In ma ya kasance mahaifiya ba za ta iya shayar da jaririnta ba saboda wani kwakwkwaran dalili, dole mahaifin yaro ya biya wata ta shayar da jaririn ko tanadar masa madara shayarwa.
Yawan Lokacin Shayarwa: Wannan shekara biyu ne kamar yadda ya zo a Ayoyi biyu masu albarka na Alkurani: Aya ta 233 Suratul Bakarah da kuma Aya ta 14 Suratul Lukman. Sai kuma Aya ta 15 Suratul Ahkaf inda aka ambaci daukar ciki da shayarwa gaba daya a matsayin wata talatin, a nan lokacin shayarwa ya kama wata 21 kenan. Iyaye za su iya zabar kowane lokaci ya yi masu matukar ba zai yi illa ga jariri ba. Kar Mahaifiya ta ce ta gaji alhali jaririnta yana ciki bukata, sai dai iyaye su duba su ga abin da ya fi alfanu ga jaririnsu kodayaushe shi za su zartar.
Tarbiyya da Ladubban Yaye:
1. Da farko bai halatta ba iyaye su wuce shekara 2 wajen shayar da jaririnsu, yin haka bijire wa umarnin Allah ne kuma yana sa yaro ya zama mara ladabi da biyayya, sannan yana kara girma yayen nasa na kara yin wuya ga mahaifiya. Don haka dole take yanke a yaye shi da zarar ya cimma shekara 2 da haihuwa. Yaye abu ne mai matukar muhimmanci ga ruhi ga ma’aikatar hankalin Jariri, hanyar farko ta ladabtar da nafsin jariri daga soye-soyen zuciyarsa domin daga shekara biyu yaro ya fara fahimtar dadin abubuwa, ba kuma abin da ya kai nono dadi a gareshi, in ba a raba shi da shi ba a daidai wannan lokacin na iya haifar masa bin soye soyen zuciyarsa, don haka yana da kyau iyaye su kula sosai kuma su dauke shi da muhimmanci.
2. bangare daya bai yin yaye, watau Mahaifiya ba ta da ikon yaye yaro ba tare da sani da amincewar mahaifi ba haka shi ma mahaifi bai da ikon tilasta Mahaifiya ta yaye yaro alhali ba ta amince ba. Dole sai sun hadu sun yi shawara su amince da lokaci mafi dacewa na yin yayen.
3. A nemi taimakon Allah Madaukakin Sarki ta hanyar yin Sallar istikhara da kuma yawaita addu’a don samun nasara da saukin yaye.
4. A tabbatar an saba wa yaro da cin abinci irin na jarinta, watau mai tsananin taushi kuma mai ruwa ruwa, a rika bashi ya ci ya koshi ta yadda ba zai ji yunwa ba har ya nemi a shayar da shi. Sannan uwa ta rage shayar da shi nono a hankali har ya zamana bai wuce sau 1 zuwa 3 yake sha ba a rana.
Za mu dakata a nan da bayani kan tarbiyya sai gaba mu dora insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.