Duniyar ma’aurata
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Ga cigaban bayani daga inda muka kwana kan ingantattun hanyoyin da ya kamata ma’aurata su bi don samar da kyakykyawar tarbiyya ga ‘ya’yansu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
*Jadawalin Kulawa: Kamar yadda ya gabata a bayanan baya, cewa mahaifiya ta samu wani dan littafi ta rika rubuta lokacin barci da tashi na jaririnta akalla na sati daya har sai ta lakanci lokutta da yanayin barcinsa da tashinsa, To haka nan ma lokacin bahanyasa, shayarwarsa, yawan rigima ko kuka, duk sai ta rubuta su a wannan littafi, da wannan bayani zata yi amfani ta yi jadawalin kulawa ga jaririnta. In ta yi Jadawalin kulawa, za ta san lokacin gabatar da komi ga jaririnta, wannan zai ba ta isashshen lokacin yin sauran ayyukanta na gida, za ta samu lokacin hutawa kuma abubuwa zasu yi mata sauki sosai. Mahaifiya ta yi taka tsan-tsan ganin cewa tsarin da jariri ya saba da shi bai canza, kamar in ana yawan tayar da shi cikin tsakiyar barcinsa zai dagula masa tsarin barcin nasa, don haka sai ayi kokari a bar shi har sai ya farka da kansa. Sannan mahaifiya ta fahimci cewa jariri na kara girma tsarin barcinsa da shayarwasa na canza, don haka sai ta runka canza wannan Jadawalin akalla duk bayan wata biyu.
Misalin Jadawalin kulawa:
8 na safe: Jariri ya farka daga barci misalin karfe 8 na safe, abu na farko shi ne inda kazanta a jikinsa a yi sauri a raba shi da ita, in kuma babu sai a dora shi a fo a yi jinkiri har sai ya yi ba-hayansa in a lokacin ya kan yo, sannan in bai yi rigima ba sai a yi mashi wanka, a shirya shi sannan a shayar da shi, in kuma yana rigima a shayar da shi tare da rirriga shi sannan a yi masa wankan. Bayan nan sai shimfide shi ya yi bari.
karfe 1 na rana: In jariri ya farka, abu na farko in bai bata jikinsa ba sai a dora shi a fo a jira har sai ya yi ba-haya a wanke masa an canza shi sannan a shayar da shi. Daga nan sai uwa ta yi wasa da shi ta hanyar yi masa tawai da rirriga shi da runguma da sumba da sauransu har, in ya bukaci shayarwa sai a shayar da shi.
karfe 4 na yamma: Zuwa lokacin sai a dora shi a fo har sai ya yi ba-haya, sannan a gyara shi a shayar da shi har sai y ayi barci.
karfe 5 na yamma: Yammaci ya kasance lokacin da jarirai suka faye rigima, don haka in jariri ya farka da rigima a wannan lokacin sai uwa ta yi hakuri ta yi ta rarrashinsa tana rirrigasa da shayar da shi har sai ya samu natsuwa.
karfe 7 na dare: Wannan lokacin sai a fara dora shi ya yi ba-haya, sannan a yi masa wankan kwanciya barci, daga nan sai a shirya shi, a shayar da shi har sai barci ya kwashe shi sannan sai a kwantar da shi.
karfe 12 na dare: In jariri ya farka cikin dare a fara dora shi a fo ya yi ba-haya ko bawali, sannan a wanke masa, a shayar da shi har sai ya koma barci.
karfe 4 na safe: Haka nan kuma za maimata in jariri ya farka gab da asuba. In kuwa bai farka ba a barsa har sai ya farka da kansa.
In Mahaifiya ta daure da yawan dora jaririnta akan fo, tun bai yin komi a ciki har ya fara, in ya saba da haka ba zai rika yawan bata kayansa ba, musamman bayan an yaye shi, don haka ice tun yana danye ake tankwasa shi, yawan amfani da abin tare ba-haya na zamani (diaper) kodayaushe yana kawo matsala ga wasu yaran bayan an yaye su ya kasance sai an yi wani sabon yayensu daga wannan sabo da aka yi masu. Wasu kuma dalilin fitsarin kwancensu ke nan. Don haka in mahaifiya ta daure ta bi wannan tsari, duk da cewa akwai wahala da cin lokaci, amma a karshe za su saukaka mata abubuwa kwarai da gaske.
Zan dakata a nan, sai Sati na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.