✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Domin kare ’yan Arewa aka kafa kwamitin tsaro a Kalaba’

An bayyana cewa domin a magance masu ci wa mutane mutunci da kai wa ’yan Arewa da suke gudanar da kananan sana’o’i haren-haren ta’adanci da…

An bayyana cewa domin a magance masu ci wa mutane mutunci da kai wa ’yan Arewa da suke gudanar da kananan sana’o’i haren-haren ta’adanci da neman samar da zaman lafiya ne ya sanya aka kafa kwamitin zaman lafiya, hadin kai da kuma tsaro a Layin Bagobiri, Unguwar Hausawa, Kalaba Jihar Kurosriba.

Shugaban kwamitin, Alhaji Ya’u Isma’il Girei ne ya bayyana haka lokacin da suka zanta da Aminiya. Ya ce:  “Matsalar kai hare-hare da ake yi wa ’yan Arewa da suke gudanar da kananan sana’o’i, ana yi musu fashi da kwace shi ya sanya aka kafa wannan kwamiti, ba domin cin zarafi ko mutuncin wani ba.”

Ya ci gaba da cewa: “Wannan kwamiti ba an kafa shi ba ne domin ya sanya a kashe wani ko cin mutuncin wani ba. Abubuwan da ake yi mana a Unguwar Hausawa, musamman yadda wasu bata gari ke rika bin mutane da ke fitowa zuwa masallaci Sallar Asuba, ana tare su ana yi masu kwace ko fashi, sai muka ga cewa wannan abu fa ya yi yawa, ya isa haka. Shi ya sa muka ce to bari mu tashi tsaye mu hada hannu da jami’an tsaro wajen magance wadannan matsaloli.”

Shugaban kwamitin ya ci gaba da cewa bayan matsalar tsaro da suke neman magancewa, “mun lura akwai wasu daga cikin jama’a ’yan kasuwa da suke sayar da miyagun kwayoyi a nan Unguwar Hausawa da hakan ke bata tarbiyyar yara. Ita ma za mu yi bakin kokari mu ga mun shawo kanta tare da magance ta kwata-kwata. Ana nan ana tattaunawa tsakanin kwamitin da jami’an tsaro, a ga yadda za a bullo wa matsalar, domin magance ta gaba daya; musamman ta masu mu’amala da sayar da miyagun kwayoyi da ma sauran kayan maye.”

Shugaban ya nemi iyaye da duk wani dan Arewa mazaunin birnin Kalaba da ya ba su hadin kai da kuma tasa gudunmawar domin samun nasara.