✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Domin kare muradun ’yan Arewa muka kafa kungiyarmu – Alhaji Hassan

Wace nasara kungiyarku ta samu a cikin shekaru 3 da kafuwarta?A baya an samu bullar kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin ’yan Arewa a wannan sashe…

Wace nasara kungiyarku ta samu a cikin shekaru 3 da kafuwarta?
A baya an samu bullar kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin ’yan Arewa a wannan sashe amma sun kasa tabuka komai a dalilin tsoma bakin wasu masu fada a ji da suka hana ruwa gudu. Amma kungiyarmu ta yi daban domin ba ta amince da shigowar irin wadannan mutane cikinta ba. Muhimmin abun da muka fara yi shi ne, hada kan matasa daga jihohi 6 na wannan sashe da muka sadaukar da kawunanmu da kudin aljihunmu wajen yi wa kungiyar rajista da mahukunta suka san da zamanta. Daga nan muka fara yin taro a kowane, wata domin tattaunawa a kan irin matsalolin da muke fuskanta kuma muka rika yin tafiye-tafiye zuwa garuruwa da kauyuka domin saduwa da mutanenmu tare da wayar da kansu da ilmantar da su a game da manufarmu da ba ta shafi bambancin kabila ko addini da siyasa ba. Duk da yake mun samu matsaloli sai dai mun gode Allah da jama’armu har da wasu shugabannin Yarabawa sun yi marhabin da manufofinmu. Wannan babban abun farin ciki ne kuma shi ne nasarar da muka fara samu a fafutukar tamu.
Me ne ne dalilin kafa wannan kungiya?
Mun kafa kungiyar ce domin lalubo hanyar kyautata zamantakewa tsakanin ’yan Arewa da ake daukarmu a matsayin baki da jama’ar gari Yarabawa da neman gwamnatocin jihohi 6 na wannan sashe su san da zamanmu da samun cin moriyar tallafin karatun zamani ga ’ya’yanmu da guraben aiki idan sun kammala karatu.  Abun bakin ciki ne ganin cewa iyaye da kakanninmu sun shafe fiye da shekaru 100 da zama a wannan sashe amma har yanzu ba mu samun guraben aiki na gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi. An mayar da mu saniyar ware wanda ba haka ake yi ga kabilun Yarabawa mazauna Arewa ba. Wannan ne ya sa muka fara shirin mika kukanmu ga sarakuna da dattawan Arewa da gwamnoni da dukkan masu fada a ji, su kawo mana dauki tun yanzu da ake da damar yin hakan ta fannin tuntubar gwamnonin wannan yanki da bayyana masu gaskiya na irin yadda kabilun Yarabawa suke mike kafafunsu a jihohin Arewa da ake ba su manyan mukaman gwamnati amma mu mun kasa samun haka a nan. Wannan babbar matsala ce da ya kamata shugabannin Arewa su warware mana domin su kadai ne za su iya yin maganin wannan al’amari.
 Ba ka ganin yawaitar kungiyoyin ’yan Arewa masu fafutukar kare hakkin dan Adam a wannan sashe za su iya yin katabus?
Babu abun da za mu iya yi a kan wannan al’amari domin ya fi karfinmu. Shugabanninmu daga Arewa su ne kadai za su iya shawo kan wannan matsala da muka dade a ciki. Abu kadan sai ka ji ana barazanar korar mutanemu daga wuraren da suke zaune, wanda ba a yin irin haka ga kabilun kudanci da ke zaune a Arewa domin ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya. Yanzu haka mun kammala shirin mika bukatunmu a rubuce ga fadar Shugaban kasa domin a ja kunnen irin wadannan mutane da suke neman raba Najeriya.
Muna iya cewa sarakunan Hausawa da na Fulani da Barebari a wannan sashe sun gaza ke nan?
Ba mu yi masu adalci ba idan muka ce sun kasa yin komai domin daga cikinsu akwai wadanda suke nuna damuwa, akwai kuma wadanda suka zama ’yan amshin shata ne. A gaskiya wasu daga cikinsu ne a kan gaba wajen lalacewar rayuwar jama’arsu a wannan yanki domin sun kasa hada kawunansu waje daya. Akwai garuruwa da yawa da ake samun sarakunan Hausawa guda 2 da sarakuna Barebari da Fulani guda 2 zuwa 3 a gari daya, wanda hakan ya taimaka wajen raba kawunan jama’arsu da kasa tafiya da murya daya zuwa ga gwamnonin wadannan jihohi da ya janyo mana koma baya.
Wadanne mutane kuka dauka a matsayin iyayen kungiya?
Sardaunan Yamma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin shi muka sanya a gaba wanda ya ba mu shawarar ziyartar sarakunan Hausawa na jihohi 6 a sashen kudu maso yamma da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da babban lauya Afe Babalola daga Jihar Ekiti da Sarakunan Bida da Borgu da Kano da Sarkin Musulmi. Duka mun ziyarci fadarsu da muka bayyana masu manufarmu da suka yi maraba da bullar irin wannan kungiya da ba a taba samun irinta a wannan sashe ba sai yanzu da muka fito.