✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dole shugabannin makarantu su rika kwana tare da dalibai — Gwamnatin Kano

Duk wanda ya bijire wa umarnin zai yi a bakin aikinsa.

Gwamnatin Kano ta sanar da cewa dukkanin shugabannin makarantun kwana na Jihar da suka bijire wa umarninta na komawa cikin makarantunsu da zama za su yi a bakin aikinsu.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Muhammad Sanusi Kiru ne ya zayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin yayin gabatar da takaradun jarrabawar neman shiga makarantun sakandire ga jami’an lura da harkokin ilimi na shiyoyin Jihar daban-daban.

A cewarsa, an bukaci shugabannnin makarantun kwana da ke fadin Jihar da su koma zama a cikin makarantun da suke jagoranta domin tabbatar da tsaro da amincin dalibai.

“Ina umartar dukkanin shugabannin makarantun kwana da su sauya shekarsu ta zama zuwa makarantun cikin gaggawa ko kuma su yi a bakin aikinsu.”

“Duk wani shugaban makaranta da yake da matsalar masauki ko mahalli a cikin makarantun ya gaggauta rubuta korafinsa ga Ma’aikatar Ilimin Jihar domin a dauki matakin da ya dace.”

“Babu ma’ana barin dalibai suna kwana a makarantu yayin da shugabanni wadanda su ne jami’ai na farko da za a tuntuba idan wata larura ta taso su kasance suna kwana a waje.”

“Akwai bukatar dukkan shugabannin makarantu su kasance suna kusa da dalibansu, musamman a wannan mawuyacin hali da kalubale na matsalar tsaro ke ci gaba da addabar kasar nan.”

“Ina so na tabbatar muku da cewa za a tanadi jami’an tsaro a dukkan makarantun domin su rika sa ido a kan duk wani motsi na shugabannin makarantun kuma duk wanda aka samu ya saba wa umarnin gwamnati zai kuka da kansa,” inji Kwamishinan.

Ya bayar da tabbaci a kan kudirin gwamnatin Jihar na tabbatar da ta katange dukkanin makarantu a fadin Jihar musamman na kwana domin tabbatar da ingancin tsaro.

Kwamishinan ya kuma bada umarnin a gaggauta tura jami’an sintiri a dukkanin makarantun kwana da ke fadin Jihar domin karfafa nagartar tsaro a cikinsu.