Kungiyoyin Ma’aikatan Jami’ar Tarayya ta kashere sun kira taron gaggawa kan cewa sai shugaban jama’ar, Farfesa Alhassan Muhammad Gani, ya tafi saboda ba zai iya shugabanci ba.
Kungiyoyin sun hadu ne da safen yau (Litinin) a babban dakin taro na jama’ar inda a halin yanzu suke tattauna yadda za ayi.
Hakan ya biyo bayan rashin biyan su albashin watan Augusta da na Oktoba saboda, wai saboda an biya su albashin watan Mayu sau biyu bisa kuskure.
A tattaunar da shugabanin kungiyoyin JAC da SANU da NAD suka yi da shugaban jama’ar, ya tabbatar musu da cewa sai sun biya wannan kudin a lokaci daya, idan bah aka ba kuma babu wani ma’aikaci da zai samu albashin watan Oktoba. Su kuma suka ce za su biya amma ba a lokaci daya ba.
Shugaban kungiyar (JAC) wato Joint Action Congress kwamred Mukthar Mohammed, ya bai wa taron ma’aikatan dama su bayyana ra’ayoyin su inda nan take suka yanke cewa kawai a kori shugaban jami’ar Farfesa Alhassan Gani.
Yanzu ma’aikatan sun nuna cewa sai an kori mataimakin shugaban jama’ar sannan kuma za a kulle Jama’ar a kulle dukkan azuzuwan karatu a kulle asibiti jama’ar sai gwamnati ta dauki matakin da ya dace an biya su albashin su sannan a bude jami’ar.
Sannan yace ba za su dawo ba har an tabbatar musu da matakin da aka dauka.