Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 30 da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa a Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa.
Kakakin ’yan sandan Jigawa, SP Lawan Shi’isu, ya ce matashin mai suna Hussaini Abubakar ana zargin ya kashe mahaifiyarsa, Dahara Mu’azu mai shekaru 75 da misalin karfe 8 na yammacin ranar 29 ga watan Yunin 2025.
- Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU
- HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina
SP Shiisu ya ce matashin ya jikkata mahaifiyarsa da bulon ƙasa, kuma bayan an garzaya da ita asibiti ta mutu washegari.
Ya ce wannan lamari ya sanya rundunar ta gaggauta tura tawagar jami’ai kuma aka cafke matashi da a yanzu haka an soma gudanar da bincike a kan lamarin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP AT Abdullahi, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin rashin imani na kololuwa.
Ya bai wa al’umma tabbacin cewa za su bi diddigin lamarin domin matashin ya girbi hukunci daidai da abin da ya aikata.
Rundunar ’yan sandan ta bukaci jama’a da su rika gaggauta mika rahoton duk wata alama ta tabin hankali ko cin zarafi domin kaucewa faruwar makamancin wannan lamarin.