Kungiyar Malamai Ta Kasa (NUT) ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta rubanya kokarinta wajen inganta walwalar malamai domin bunkasa harkar ilimi a kasa baki daya.
Shugaban NUT, Nasir Idris, wanda ta bakin Sakataren Watsa Labaran kungiyar, Amba Audu ya ce muddin aka biya musu su wasu bukatu guda biya, to harkar ilimi zata bunkasa.
“Bukatun namu sun hada da kara yawan shekarun ritayar malamai da sauran jami’an ilimi, kirkiro da sabon tsarin albashin malamai da sauran abubuwan da za su farfado da harkar,” inji shi.
A jawabinsa na zagayowar Ranar Malamai ta Duniya ta 2020 Idris ya ce sauran bukatun su ne kafa Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Kasa, kaddamar da sabon tsarin mafi karancin albashi da kuma aiwatar da ware kashi 27.5% na alawus din malaman makarantun hadaka na Gwamnatin Tarayya.
Shi kuwa a nasa jawabin, minista a ma’aikatar ilimi, Chukwuemeka Nwajuba ya ce gwamnati ta kirkiro da wata kyauta da za a rika ba malaman da suka yi zarra tsakanin takwarorinsu a harkar koyarwa.
Ya ce tuni aka aike wa dukkannin jihohi da Birnin Tarayya ka’idojin zabar wadanda za su shiga gasar, ko da yake jihohi 24 ne kawai suka aiko da sunayen ya zuwa yanzu.
Kyautukan da za a bayar guda biyar ne kuma sun hada da na makarantar gwamnati da ta yi zarra, makaranta mai zaman kanta da ta yi zarra, fitaccen malamin makarantar gwamnati, fitaccen malamin makaranta mai zaman kanta sai kuma fitaccen mai kula da makarantun gwamnati.