Fitaccen Bafulatanin dan siyasa kuma manazarci a fannin Tarihi, Dokta Umar Ardo, ya gargadi Shugaba Muhammadu Buhari kan yiwuwar barkewar rikicin kabilanci matukar bai sa an kama wanda suke rura wutar tayar da zaune a kasar ba.
Ardo ya yi wannan gargadi sakamakon wani hoton bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, wanda ke nuna yadda wasu mutane da ake zargi masu fafutikar kafa yankin Biyafara ne suke kai wa wasu Fulani farmaki tare da kone musu dukiya da kuma kashe shanunsu.
- An kashe mutum daya a rikicin Fulani makiyaya da manoma a Ogun
- Saraki ya gargadi Buhari kan rikicin Fulani da Yarbawa
- Rikicin Fulani: Sule Lamido ya kare Buhari
- Yadda aka kai wa Fulani hari a Oyo
A cewarsa, “Akwai bukatar Shugaba Buhari ya tashi ya farga a yayin da galibi Fulani makiyaya ke ci gaba da ta’adar garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe da kuma maganganun tunzura da kungiyoyi irinsu Miyetti Allah ke kara ta’azzara.”
“Ya kamata shugaba Buhari ya shirya taron Majalisar Koli don tattaunawa a kan hanyoyin magance wannan rikici da ke tasowa, matukar ana so Najeriy ta ci gaba da zama lafiya,” inji Dokta Ardo.
Ardo, wanda tsohon dan takarar gwamna ne a Jihar Adamawa ya bayyana haka ne yayin zantawarsa da Aminiya, inda ya bukaci Shugaba Buhari ya mike tsaye domin dakile barkewar rikicin kabilanci a kasar.
Yayin da yake Allah wadai da ayyukan ta’addancin da wasu daga cikin kabilar Fulani ke yi, ya kuma ce irin kiyayyar da ake nuna wa Fulani a kasar nan ba zai haifar da da mai ido ba.
Wasu na fake wa da rigar kabilar Fulani
Jigon jam’iyyar PDP, ya ce wasu gungun bata gari da suke fakewa da sunan Fulani wajen aikata manyan laifuka da suka hada da garkuwa da mutane kasha-kashe, na neman amfani da wannan dama wajen kawo rikici a Najeriya.
“Wasu masu tsattsauran ra’ayi daga cikin Fulani ana amfani da su wajen cimma wata mummunar manufa.”
“A hankali lamarin yana sauya akala daga sace-sacen mutane da Fulani ke yi zuwa kashe su kansu Fulanin, wanda kuma yana neman zama fadan kabilanci.”
“Abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a Kudu maso Yamma, da Kudu maso Gabas, abun ba a cewa komai,” in ji Ardo.
Dokta Ardo ya koka kan yadda gwamnatin tarayya ta yi shiru kan lamarin, inda yake kira ga Shugaba Buhari da sauran manyan ‘yan Najeriya da su nemo hanyar magance matsalar tun kafin ta wuce gona da iri.