Uban jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya ce ya zama tilas duk masu neman shugabancin kasar nan da sauran masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa domin jam’iyyar ta ci gaba da rike madafun iko a zaben 2023.
Tinubu, wanda daya ne daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya bayyana haka ne a yayin taron jam’iyyar na musamman da aka gudanar a daren ranar Talata a dandalin Eagle Square da ke Abuja.
Ya ce dole ne magajin Shugaba Buhari ya kasance yana da gogewa da himma wajen tafiyar da al’amuran al’adu daban-daban na kasar nan kan tafarkin daukaka.
Tinubu ya ce tarihinsa na shugabancin kamfanoni, kwarewa ta fannin gudanar da kudi da gogewarsa a matsayinsa na Gwamnan Kihar Legas ya sa ya bambanta a cikin masu son tsayawa takara.
Ya bayyana cewa hakan ya ba shi kwarewar da ake bukata don hanzarta sauye-sauyen ci gaba da za su sauya fasalin tattalin arzikin kasa.
Ya ce, “Wannan babban taro kuma ya kawo karshen zangon farko na zabukan 2023.
“Zaben fid-da gwani daya ne daga cikin gasa mai tsanani tsakanin wadanda ke da burin tsayawa takara.
“Ina yaba wa sauran ‘yan takara bisa irin martaba da kishin da suka gudanar da yakin neman zabensu, irin hakan zai sa jam’iyyarmu ta yi nasara.
“Dole ne mu fito daga yau (Talata) rundunar hadin gwiwa ta mayar da hankali kan hadin gwiwa da nasara.
“Kamar yadda shugaba Buhari ya ce, dole ne burin jam’iyyar mu shi ne samun nasara a zaben badi a dukkan matakai.
“Dole ne dan takarar da kuka zaba ya zaman wanda zai iya babban zaben kasa kuma ya yana da kima da kishin kasa da zai jawo mu ga nasara a zabukan jihohi da na kananan hukumomi, shi ma ya sanya tunanin samun nasara da kwarin gwiwa.
“Bugu da kari, dole ne dan takarar ya hada kan ‘yan Nijeriya daga kowane bangare na rayuwa, daga sassan kasar nan.
“Dole ne ya zama yana da gogewa da iya jagoranci, ilimi, da kuma tuntubar mutane don tafiyar al’amura, ya san mutane a sassan Nijeriya , musamman a irin wannan lokacin kalubale da duniya ke fama da shi.
“Sauran ‘yan takarar duk mutanen kirki ne. Amma na yi imani cewa ni ne mutumin da ya fi dacewa..
“Ina da gogewa. Na kawo sauyi a Jihar Legas daga wuri mai hatsari, wanda ba a yarda da shi ba a 1999 zuwa wuri mai tsafta, aminci, kyau da kuma matsayi na biyar mafi girma na tattalin arziki a duk Afirka.
“Ni mutum ne mai kishin kasa mai manufa kuma zan yi amfani da duk abin da na sani da kuma dukkan karfina wajen amfanar jama’a.
“Ni shugaba ne mai ba da hadin kai wajen gina tsarin siyasa mai ban sha’awa, wanda ya samar da nasarar zabe bayan nasarar zabe.
“A yanzu ban saka kaina a gaba ba saboda ina ganin wannan nadin ya dace na.
“Ina neman takarar ce saboda na yi imanin zan iya jagorantar jam’iyyar mu zuwa ga kyakkyawar makoma.”