✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole mu ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin ’yan ta’adda — Tinubu

Tinubu ya ce waɗanda suke sace yara matsorata ne da ba za su iya gaba da gaba da sojojin Najeriya ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce daga yanzu duk wasu masu aikata kazamin laifi na garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa za a ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake buɗa-baki da alƙalan gwamnatin tarayya a ranar Talata, ƙarƙashin jagorancin Alƙalin-Alƙalai na Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.

Shugaban Kasar ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na fatattakar ’yan bindiga, yana mai cewa waɗanda ke yin garkuwa da yara matsorata ne da ba za su iya tunkarar ƙarfin sojojin Nijeriya ba.

A sanarwar da mai magana yawunsa, Mista Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya ce waɗanda suke sace yara matsorata ne da ba za su iya gaba da gaba da sojojin Najeriya ba.

‘“Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin ’yan ta’adda. Duk da cewa matsorata ne kuma wulaƙantattu ne su. Suna kai hari kan marasa rauni.

“Suna zuwa makarantu suna sace yara suna haifar da rashin jituwa. Dole ne mu ɗauke su daidai a matsayin ’yan ta’adda don mu kawar da su, kuma na yi muku alƙawarin za mu kawar da su,” in ji Tinubun.

Waɗannan kalamai na Tinubu na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumomi sun ceto ɗaliban firamare da ƙaramar sakandire da aka sace a garin Kuriga na Jihar Kaduna mako biyu da suka wuce.