Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika ya ce wajibi ne masu shigowa Najeriya daga kasashen waje su yi gwajin COVID-19 ‘yan kwanaki kafin shigowarsu.
“Za a bude shafin intanet da fasinjojin za su biya kudin gwajin COVID-19 da za a yi musu bayan kwana takwas da isowarsu Najeriya”, kamar yada kakakin ministan, James Odaudu ya ruwaito shi.
Ya kara da cewa fasinjojin “za su kuma cikie takardar bayanan lafiyarsu ta intanet, sannan su mika su da zarar sun sauka a Najeriya, maimakon cikewa a cikin jirgi ko bayan saukarsu a Najeriya.
Za kuma a ci gaba da bin sauran matakan kariya da suka hada da “ba da tazara, sanya takunkumi da wanke hannu da kuma gwada zafin jiki”.
Tun da farko ministan ya sanara da bude jigilar jiragen sama na kasa da kasa daga ranar 29 ga watan Agusta, bayan kusan wata hudu suna rufe.
Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shirye-shirye sun yi nisa na dawo da harkoki a tashohin.