More Podcasts
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan
Daga yau, saura kwanaki biyu kacal Bola Ahmed Tinubu ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya.
Shugaban mai jiran gado zai taho da sabon shirin habaka tattalin arziki, da bunkasa hanyoyin samar da abincin da Najeriya za ta iya dogaro da kanta, da kuma buda wa matasa tare da ba su damar yin rawar gaban hantsi.
Ko me Gamayyar Kungiyoyin Mutanen Arewa za ta ce game da wannan? A ganinta ta yaya sabon shugaban zai iya cimma wannan sabon buri duba da irin matsalolin da ke gaban gwamnatinsa?
Shin akwai wasu abubuwa na takamaimai da ya kamata gwamnati mai zuwa ta sani game da Arewa?