✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dole Asibitocin Kaduna su koma karbar kudi ta POS —Gwamnati

Gwamnatin Kaduna ta ce za ta samar da wadatattun cibiyoyin POS a asibitocinta domin saukaka wa mutane biyan kudi

Gwamnatin Jihar Kaduna ta umarci asibitocinta su koma karbar kudi ta na’urar POS, duba da yadda ake fama da karancin takardun kudi a Najeriya.

Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta ce tana kokarin samar da wadatattun cibiyoyin POS a asibitocin gwamnatin jihar domin saukaka wa mutane biyan kudi.

Da yake jawabi bayan korafi jama’a cewa asibitocin Gwamnatin Jihar Kaduna na tilasta wa mutane biyan tsabar kudi, duk kuwa da karancinsu da ake fama da shi, Shugaban Hukumar, Dokta Ziad Abubakar, ya ce gwamnatin jihar ta riga ta soke biyan tsabar kudi a asibiti.

A cewarsa, “Tun kafin sauyin kudi Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta biyan tsabar kudi a asibitocinta, karkashin sashe na 51 na Dokar Hadewa da Biyan Haraji ta Zamani ta 2020.

“Saboda haka babu hujja wani asibitin gwamnati ya ki karbar biya ta na’urar zamani.”

Daga nan ya kara da cewa, a halin da ake ciki na karancin takardun Naira, hanya mafi sauki ita ce konawa amfani da hanyoyin zamani wajen yin cinikayya.

%d bloggers like this: