Tsohon dan takarar Shugabancin Kasa a Jamhuriyya ta uku, marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa, ya ce idan har ana so a samu sauyi a tsarin siyasar Najeriya, to dole sai an shafe tarihin jam’iyyun siyasar da ake da su a halin yanzu.
Ya ce za a iya yin hakan ne ta hanyar kafa wasu sabbin jam’iyyun masu karfi.
Marigayin ya fadi hakan ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a gidansa da ke Kano, kwanaki kadan kafin rasuwarsa.
Alhaji Bashir Tofa ya ce ba wai kawai jam’iyyun za a canza ba, har ma mutanen da za su yi mulkin.
“Idan zai yiwu a samar da sabuwar jam’iyya mai karfi ko kuma a hadu a mara baya ga wata jam’iyya daga cikin kananan jam’iyyun da muke da su.
“A canza mutanen da suke yin mulkin koyaushe. A gwada wasu mutanen domin a ga kamun ludayinsu.
“A yi watsi da wadannan shirmen APC da PDP. A ajiye mutanen da suka dade suna mulki a gefe.
“Wannan gwamnan nan da ya yi sau biyu a jiye shi Sanatan nan da yake ta yi shi ma a ajiye shi a gefe. A samu wasu sabbi a zuba su a mulkin.”
Marigayin ya bayyana cewa akwai jan aiki a gaban ’yan siyasa wajen kawo sauyi domin dole sai sun ajiye halayyar kwadayi da tumasanci sun tsaya da kafafuwansu.
“Babu wani abu na kwarai da ke samuwa cikin sauki, don haka akwai bukatar ’yan siyasa su fito su yi jihadi su samar da mutane nagartattu wadanda za su kai al’umma ga tudun mun tsira, amma ba wai a zauna a yi ta surutu na neman sauyi ba tare da daukar mataki ba.”
Barawonka, gwaninka
Ya yi kira ga matasa da su ajiye siyasar jagaliyanci su fuskanci siyasar akida.
“Akwai bukatar matasanmu su daina siyasar kudi da jagaliyanci. Su fuskanci siyasar akida wacce za ta kai su ga samun sauyi mai nagarta .
“Ya kamata matasa su dawo daga rakiyar ’yan siyasar da ke dora su a hanyar lalacewa. Su yi kokari su kawar da kansu da zuciyarsu daga kwadayin abin da suke samu daga hannun wadannan ’yan siyasar su tsaya su yi abin da ya dace wajen mara wa nagartattun mutane baya don samun shugabanni na gari.
“Idan ban da ma wauta ta yaya za ka rika yaba wa barawonka; mutumin da ke satar dukiyarka shi ne kuma gwaninka?
“Akwai bukatar ku yi karatun ta nutsa, ku daina bin wadannan mutanen suna ingiza ku kuna dabanci kuna kashe junanku a banza a duniya sannan idan kun je lahira ku hadu da azabar Allah.”
Ku kasance da jaridar Aminiya ta ranar Juma’a domin karanta cikakkiyar hirar.