Cif Edwin Clark an zabe shi a matsayin kansila a shekarar 1953. Sannan ya zama Kwamishina a Gwamnatin Yamma ta Tsakiya, ya zama Minista a mulkin soja na Yakubu Gowon sannan Sanata a Jamhuriyya ta Biyu.
A tattaunawa da jagoran na kabilar Ijaw wanda ke da sha’awar siyasar Najeriya ya yi magana a kan yarintarsa zuwa karatunsa da kuma rayuwarsa.
Yaya za ka bayyana kuruciyarka a wancan lokaci?
An haifi ne a ranar 25 ga Mayun 1927. Kanina marigayi Farfesa JP Clark an haifi shi ne a 1930.
Ban san yadda iyayena suka yi tazarar haihuwarsu ba, amma mahaifiyata tana haihuwa ce bayan shekara uku.
Mun girma tare da kakarmu bayan ta rasu sai baffanmu Gori ya dauke mu wanda masunci ne. A lokacin ina dan shekara 10.
Baffanmu yakan tafi kamun kifi cikin dare zuwa wayewar gari da safe sai mu je bakin rafi kwaso kifin.
Wata rana, daya daga cikin kifin da ke raye ya fada cikin ruwa a lokacin da nake kokarin kwashewa.
A kan hanyarmu ta komawa sai baffana ya tambaye mu me ya faru sai na fada masa ai kifin ya koma cikin ruwa sai ya fada min ai zai sake kama shi.
Bayan wani lokaci, sai mahaifinmu ya ga ya dace mu fara karatun boko. Sai ya tura mu wurin mahaifiyarsa domin karatu, a makarantar malami daya ne ke koyar da mu a Elemantare har zuwa aji hudu.
Wata rana ya kira mu ya ce yana wahala wajen furta sunanmu. Sunana Kiagbodo shi kuma kanina sunansa Akporode. Dayan ana kiransa Pepe.
An rada masa sunan daya ne daga cikin ma’aikatan da ke zuwa unguwanmu. Ya ce furta Pepe ba ya masa wahala, amma sai ya ce zai ba mu sunan Turawa.
Ya kira dukkanmu hudu ya ce mana daga wannan rana zan koma Edwin Clark shi kuma dayan Godwin Clark sannan ’yar uwata kuma Blessing Clark.
Dan karaminmu kuma aka sa masa suna Johnson Clark. Haka muka samu sunayenmu.
Ke nan ka samu shiga makaranta har ka zama malami?
Eh, muna tare da kakarmu a kasar Urhobo amma mahaifinmu na son mu koma makaranta a yankin Ijaw.
Saboda haka sai ya kai mu wani wuri da ake kira Okereka-Gana-Gana, wani yanki mallakar Kamfanin Niger.
Makarantar da muka je mallakar En’e ce (Natibe Authority) an kafa ta ce a 1937.
Mahaifinmu ya ce ba ya son mu zauna tare da kowa hakan ya sa muka yi zamanmu mu kadai.
Babu abin adana dumi a zamanin hakan ya sa idan muka dafa abinci sai mu raba don gudun kada a cuci wani. Idan mun ci abinci sai mu kwashe tukwane zuwa bakin rafi mu wanke.
Idan muka sa kwanukan a cikin ruwa sai ka ga kifi ya shiga ciki daga nan sai mu je mu gasa mu ci.
A lokacin ban san kifin da ake ajiyewa a firiji ba ko da dan uwana ya kawo min ba na ci saboda ban saba ci ba. Amma abin bakin ciki a yau saboda ayyukan kamfanonin mai duk kifayen sun mace.
A wancan lokaci muna yara a yankinmu mukan yi iyo a cikin ruwa ko da kuwa manyan jiragen ruwa sun zo wucewa.
Sannan muna tuka kwalekwale, amma ba za ka iya yin hakan ba a yanzu saboda ayyukan kamfanonin man fetur.
Akwai abinci masu yawa a lokacin sannan ga ruwan sha mai kyau. Ba sai ka sayi ruwan roba ba sai dai kawai ka je bakin rafi ka diba ka sha. A lokacin rayuwa na da dadi.
Yaushe ka zama malamin makaranta?
Bari in fada maka cewa a 1945 wadanda suka kammala karatunsu na elemantare bayan shekara takwas sai a ba su satifiket amma a lokacinmu Jihar Kudu maso Yamma ta fito da tsarin jarrabawa ga kowace makaranta.
Mu tara ne a aji, a cikinmu biyar sun ci jarrabawar a wasu makarantun dalibai biyu ne suka ci a wasu kuma dalibi daya a gaba daya yankin.
Mahaifinmu ya ce in tafi kwaleji a Warri don haka sai na tafi jarrabawar gwaji.
Cif Eruku ne akawun ilimi a lokacin bayan na yi magana da shi sai suka bayyana min cewa “Abin bakin ciki, ba za mu iya daukarka ba. Kana da kani? Na ce eh, sai suka ce in je in koyar a aji saboda wai na riga na girma. Sun ce wai in koyar a Makarantar Gwamnati ta Abracara.
Daga nan sai suka ce na dace, amma kuma wai na yi kankanta. Da na je sakandare na yi girma, amma a kwalejin koyar da malanta sai aka ce na yi kankanta sai aka ba ni wasika in je in koyar.
Ka ji yadda aka yi na zama malamin makaranta a makarantar da na gama.
Bayan shekara daya sai na koma kwaleji kuma a lokacin sai ka kwashe shekara biyu kafin ka samu satifiket sannan ka fito ka je koyon sanin makamar aiki shekara biyu.
Amma wani shugaban makaranta daga Birtaniya da ya zo ya ce bayan shekara biyu duk za mu tafi. Sai na koma tsohuwar makarantarmu na zama Shugaban Makarantar.
Bayan shekara daya sai aka sake nema na. Wasu daga cikin dalibaina sai muka zama ’yan aji daya tare sannan abokan karatuna a baya suka koma kasa da ni.
A 1953 na ci jarrabawata ta kammala shaidar malanta na zama shugaba mai cikakken iko. A matsayina na shugaba an rika tura ni wurare daban-daban aiki.
Ko a lokacin ne aka zabe ka kansila?
Lokacin da nake shugaban makarantar Bamodi sai Awolowo ya amince da tsarin kananan hukumomi a 1952 da 1955. A shekarar 1955 na tsaya takara a karamar hukuma.
Ni da mahaifina muka zama kansaloli a karamar hukuma daya. Wata rana mahaifina ya gabatar da wani kudiri kowa ya goyi baya, amma na ki amincewa da shi. Kowa ya kalle ni.
Wani Bature mai suna Mista Patrick yana wajen lokacin da ake tattaunawa kuma shi ma ra’ayinsa ya bambanta da na mahaifina.
Mahaifina ya yi min tsawa “Kada ka kuskura ka zo gidana daga yau. Kana kalubalantana a cikin mutane!”
Sai da na kwashe wata uku ban sa mahaifina a ido ba, amma daga bisani na dawo gida inda ya ce ai tuni ya mance da abin da ya faru.
Ya tambaye ni me ya hana ni dawowa gida na ce ai ina aiki ne.
Yaushe ka samu gurbin zuwa kasar Birtaniya?
Abin da ya faru shi ne na zama dan siyasa sosai har na zama shugaban al’umma a yankinmu duk da kasancewata matashin shugaban makaranta.
Lokacin da na nuna ba na son ci gaba da zama shugaban makaranta sai na ci gaba da ba da gudummawata a garinmu.
Gwamnati ta yi sanarwa a kan tana neman jami’in al’umma sai na nema kuma aka nada ni. Aka kai ni Ogaciku. Wannan ne sanadin barin karantarwata.
Aikina shi ne shiga garuruwa ina ilimantar da mutane yadda za su dogara da kansu kafin gwamnati ta shigo ta taimaka musu.
Idan kana son zama dan kasuwa ne sai ka fara kasuwanci daga nan sai gwamnati ta zo ta tallafa.
Muna kiran aikin Ci-gaban Al’umma sai aka kai ni yankin Warri a matsayin shugaba na kuma ilimantar da jama’a masu yawan gaske.
Na tuna a 1959 ko 1960 akwai wata kungiyar zaman lafiya ta kasar Amurka wadda matasan Amurka kusan 20 aka turo su yankin Delta aka kuma damka su a hannuna.
Sun zo ne su magance wa mutanen garin ambaliya, sai yawancin mutanen suka nuna adawarsu da farko amma daga baya suka amince.
Na fada masu cewa sai mun sayi siminti kafin gwamnati ta taimaka kuma da muka fara sai gwamnatin ta kawo mana dauki.
Wannan abin da muka gina a 1960 yana nan har yanzu yana tare ambaliya daga shiga cikin kauyen. Amurkawan sun kwashe mako uku ne a garin.
A 1960 na ci jarrabawar GCE. Na ce ina son tafiya kasar waje don yin karatun lauya saboda a zamanin ina raka kakana kotu.
Na girma ina ganin manyan lauyoyi na zuwa Warri domin yin shari’a ba a yanzu da wasu lauyoyin ba sa kama da lauya ba.
Wannan abin ya ba ni sha’awa saboda haka a 1961 na bar kasar nan zuwa Ingila na kuma zama karamin dan siyasa ne saboda kasancewata dan Jam’iyyar NCNC.
A lokacin da nake Ingila an ajiye mu ne a yankin Hans Crescent a Knight Bridge, inda muke tare da su Liberty daga Maiduguri wanda babban lauya ne da kuma Alkali Kaltungo na Kotun Koli da Hassan Adamu Wakilin Adamawa sai kuma Abdullahi Ibrahim tsohon Lauyan Gwamnati da Ibrahim Tahir wanda shi bai zauna a Hans ba, amma yana ziyartar mu.
A lokacin da nake Kwalejin Malanta ina sayen jaridar Daily Times da alawus dina saboda sauran dalibai su rika zuwa wurina suna karatu.
Na tuna Gwamnan Kudu ya ziyarci makarantarmu, inda muka taru ya yi mana jawabi. Na tambaye shi me ya sa mutane irin su Azikiwe da Cif Awolowo ba su da shaidar girmamawa ta OB da NBA, amma sai a ba wa sarakuna. Ko don saboda su ’yan siyasa ne?
Mutumin ya so ya amsa tambayar, amma sai shugaban makarantarmu ya ce kada ya amsa.
Da yamma mun taru a dakin cin abinci na dalibai sai daya daga cikin shugabannin dalibai ya tara mu domin yi mana jawabi.
Ya ce in tashi tsaye a kan wani teburi, na yi abin da ya umarta. Ya ce tunda har zan iya yin tambaya dole a hukunta ni ta hanyar wanke kwanukan dalibai na kwana uku. Kuma sai da na yi hakan.
Daga baya kuma sai malamin da ke koyar da mu harkokin noma shi ma ya kira ni cewa akwai wata kyauta da zai ba ni saboda sun ji dadin abin da na yi. Amma ban fada masa cewa an sa ni wanke kwanuka ba saboda abin da na yi din.
Me ya faru a Ingila?
Akwai dalibai daga kasar Austireliya da Kanada da sauran kasashen Turai kuma ni ne wakilinsu.
Daga karshe sun zabe ni in zama shugabansu. Ni ke wakiltarsu a duk al’amuran da suka shafe su a Birtaniya. Sun sake zaba ta a karo na biyu. Ka ji yadda na fara siyasa.
Na zama Sakataren Vanguard da Sakataren Yamma ta Tsakiya da sauransu. Saboda haka na kasance cikin siyasa na tsawon lokaci.
A kasa irin Najeriya mai tafiya a tsarin tarayya a ina dukiyar yanki ta kamata ta kasance?
Kamar yadda kundin Tsarin Mulki na 1963 a Sashe na 400 an bayyana cewa kashi 50 na dukiyar yanki za su ajiye abinsu.
Sannan kashi 20 kuma a kai wa Gwamnatin Tarayya ta gudanar da ayyukanta. Sannan sauran kashi 30 kuma sai a raba a tsakanin Gwamnatin Tarayya da sauran yankuna uku.
A kwanan nan, na rubuta kasida inda na yi bayanin cewa a tsarin tarayya, Arewa da Kudu maso Gabas da Kudu Maso Yamma su suka samar da Najeriya.
Idan daya daga cikin wadannan kafafu ya samu matsala za a samu matsala. A yanzu muna da kafafu 36 an kuma canza komai daga tattalin arziki zuwa na al’umma.
Fada da nake yi a yanzu shi ne a koma ga kundin Tsarin Mulkin 1963 saboda abubuwan da suke faruwa a yanzu.
Amma kamar ba ka jin dadin yadda ake siyasa a Najeriya a yau, akwai wani bambanci ne da ka lura da shi?
Daya daga cikin matsaloli da muke fama da su, su ne muna ganin idan har za mu kasance a kasa guda dole dukiyar kasa ta zama ta kowa.
Daga 1953 zuwa 1966 da muke tare da Yamma Awolowo ya kawo kamfanin gini daga kasar Isra’ila domin yin titi a yankin. Babu daya daga cikin ’yan kwangilar daga yankin Yamma ta Tsakiya.
An fara kawo talabijin a 1959, amma ba a kawo yankin ba. Lokacin da aka kirkiri yankin Yamma ta Tsakiya a 1963 Kudu maso Yamma ta ki raba kadarori da dukiya saboda ba mu ba da gudummawa ba a ci gaban Yammancin Najeriya.
Har na zama kwamishinan kudi yankin Yammaci a karkashin jagaroncin Janar Adebayo ya ce ba mu ba da wata gudummawa ba a ci gaban tattalin arzikin yankin.
Ban yarda da hakan ba domin kowace jiha kamata ya yi ta samu. Ni ba ni da wata matsala da ’yan Arewa da ke da bukatar man fetur, amma akwai bukatar su girmama mutanen da ke da dukiyar.
A yau kashi 99 na mutanen da suka mallaki rijiyoyin man fetur ’yan Arewa ne da ’yan Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma. ’Yan Kudu maso Kudu kuwa ba su da ita. Babu adalci a nan.
Kana ganin saboda adalci akwai bukatar mulki ya koma Kudu?
Eh a yanzu ba.
Kana ganin za a cim ma wannan buri a yanzu da jam’iyyu suka tsayar da ’yan takara?
Na ji dadi da ka yi wannan tambaya. Bari in fada maka cewa ko kakanninmu sun tabbatar da cewa ba daidai ba ne yanki guda ya kwashe duk mukamai.
Lokacin da Tafawa Balewa ya zama Firayi Mista Nnamdi Azikiwe ne ya zama Gwamna-Janar.
Bari kuma in fada maka cewa a lokacin da sojojin Birtaniya ke janyewa suna son dan kasa ya hau sai suka dauko Ironsi da Maimalari.
Maimalari ya fi Ironsi kwarewa don haka suka nemi su ba shi, amma sai Ministan Tsaro a lokacin ya ce bai da ce ba a ba shi mukamin Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasa ba.
Ka ji yadda Ironsi ya samu mukamin. Sun yi amfani da hankalinsu.
Amma a yanzu a lokacin Buhari sai suka kwashe komai a bangare daya. Suna neman su mallake komai ai hakan ba adalci ba ne.
A lokacin da Obasanjo ya hau mulki babu wani batun juya-juya amma na tuna yadda aka raba mukamai a lokacin da nake dan Jam’iyar NPN.
Kujerar Shugaban Kasa aka mika ta Arewa. Shugaban jam’iyya aka kai Yamma, Sakatare kuma aka kai Gabas, Mataimakin Shugaban jam’iyya kuwa aka kai Kudu maso Kudu.
Ni ne shugaban gudanar da zaben fid-da-gwani, zaben fid-da gwani na gaskiya ba irin wanda aka yi a yanzu ba.
Shagari ya gudunar da zaben fid-da gwani na gaskiya bayan shekara hudu.
Kafin a zabi Shagari sai da muka je Kaduna taro, inda aka amince cewa bayan ya kammala shekara takwas mulki zai koma Kudu.
Sako ne ga yankin Yamma da yankin Gabas cewa daya daga cikinsu ne zai samar da Shugaban Kasa da zai maye gurbin Shagari.
Abin bakin ciki sai juyin mulkin ya auku a lokacin domin bai kamata ya faru ba.
A 1999 Obasanjo da Olu Falae sun yi takarar saboda suna son adalci da daidaito idan aka yi la’akari da abin da ya faru da MKO Abiola a lokacin.
Daga karshe Atiku Abubakar ya nuna kwadayinsa, inda ya nemi ya gaji Obasanjo amma hakan bai yiwu ba.
Aka kawo Umaru ’Yar’aduwa amma abin bakin ciki sai ya rasu. Mutumin kirki ne mai saukin kai.
A shekarar 2011 ’yan Arewa suka ce lokacinsu ne saboda ’Yar’aduwa bai kammala wa’adinsa ba. Goodluck Jonathan ya yi takara, amma duk ’yan Arewa suka rika ganin wai wa’adinsu ne har da mafi rinjayen kabilun yankin.
Abin mamaki ka yi aure kana da shekara 86 wanda ya sa mutane suka rika surutai. Me ya sa ka yi haka?
A matsayina na mutumin mutane ne na bukaci yin hakan. Maza da mata na kaunata ni ma kuma ina kaunarsu. Da gaske ne na yi hakan.
Ina kaunar halittun Allah saboda haka a lokacin da na hadu da kyakkyawar matashiyar likita, sai na kamu da soyayyarta na kuma aure ta.
Ba na bukatar haihuwa ita ma ba ta bukatar haihuwa .
Fassarar Mohammed I.Yaba, Kaduna