Kasar Saudiyya ta ce daga wata mai kamawa dole ne a rika yi wa dukkan mutanen da ke aiki a bangaren Aikin Hajji da ma maniyyata rigakafin COVID-19 ko kuma a rika yi musu gwajinta a a kowanne mako.
A kowacce shekara dai miliyoyin Musulmai ne ke gudanar da ibadar Aikin Hajji da Umara a kasar.
- ‘Babu mahalukin da ya isa ya karya Gwamnatin Buhari’
- Sam Buhari bai fahimci zanen gadar da Ganduje ya kai masa ba – Kwankwaso
Sai dai sakamakon bullar annobar Coronavirus a bara, kasar ta sanar da soke aikin Hajjin ga ’yan kasashen waje inda ta kyale mazauna kasar kadai suka gudanar da aikin.
A ranar Juma’a ne dai Ma’aikatar Aikin Hajji da Umara ta kasar ta sanar da hakan inda ta ce umarnin ya kuma kunshi masu shaguna da sauran ayyuka a wuraren ibadar.
Daga farkon watan azumin Ramadan ne ake sa ran fara aiki da sabuwar dokar.
To sai dai har yanzu kasar ba ta sanar da adadin mutanen da za su gudanar dsa Aikin Hajjin na bana ba.
Ko a farkon watan Maris dai sai da kasar ta sanar da wajabcin yi wa dukkan masu son shiga kasar domin Aikin Hajji ko Umara yin rigakafin cutar ta COVID-19.
Ya zuwa yanzu dai, an yi wa akalla mutane miliyan uku daga cikin sama da mutane miliyan 35 dake kasar.